Coronavirus: Gwamnatin Birtaniya ta dauki gagarumin mataki

An wallafa

Bayan tafiyar hawainiyar da gwamnatin Birtaniya ta yi kan dakile bazuwar coronavirus, a yanzu ta fitar da wani shirin da zai shafi 'yancin walwalar 'yan kasar.

Cikin matakan da gwamnatin ta bayyana, ana bukatar dukkan mutanen gidan da wani daga cikinsu ya nuna alamar kamuwa da cutar - ta hanyar tarin da ya ki warkewa ko zafin jiki - da su killace kansu na kwana 14.

Gwamnatin ta Birtaniya ta nemi dukkan 'yan kasar da su daina cudanyar kusanci da juna -- wato su daina zuwa shaguna da mashaya da silima da sauran wuraren da jama'a kan taru.

Ta kuma umarci gidajen da ke kula da tsofaffi da su hana baki shiga ganin tsofaffin da ke cikin gidajen.

Wannan kuma na nufin za a dakatar da dukkan wasanni kamar na kwallon kafa da cricket domin yadda dubban mutane kan taru a filayen wasa.

Ana kuma bukatar yawancin mutanen Birtaniya da koma yin aiki daga gida, musamman a birnin Landan - birnin da ake tsammanin kwayar cutar ta bazu fiye da sauran kasar.

A wata ganawa da manema labarai da Firai Minista Boris Johnson ya yi -- inda daga yanzu zai kasance kullum zai rika yin wannan ganawar - ya bayyana dalilansa na sauya takun da gwamnatinsa ke yi kan yaki da cutar.

Firai Ministan ya ce "Ina fatan 'yan kasarmu za su aiwatar da matakan nan da kashin kansu, ba sai gwamnati ta tilasta musu kulle gidajen abinci da sauran wurare ba."

Amma ya ce babu wani shiri na kulle makarantu a yanzu, sai dai yana ganin wannan na iya sauyawa idan lamarin ya bukaci haka.

Ya kuma ce akwai shirin ayyana dokar ta baci.

Babban likitan gwamnatin Birtaniya Farfesa Chris Whitty ya gargadi wadanda ke killace kansu tare da wanda ke dauke da cutar:

"Ku sani cewa kuma za ku iya kamuwa da wannan cutar, amma matakin naku ya zama tilas ku dauke shi domin kare sauran al'umma daga kamuwa".

Ya ce yau gwamnatin kasarmu ta wallafa matakai mafi tsauri domin yakar wannnan annoba:

A ciki ya ce akwai nesanta mu'amula da abokai da 'yan uwa da shiga motar haya. Ya kuma ce mata masu ciki da tsofaffin da shekarunsu suka kai 70 da masu fama da rashin lafiya su ma su dinga zama a gida.

Amma shugaban jam'iyyar Labour Jeremy Corbyn wanda shekarunsa 70 da haihuwa, ya soki matakan gwamnatin, inda ya ce ba za su biya bukatun 'yan kasar ba.

Kuma ya ce duk da cewa ya tsufa, ba zai zauna a gida ba, amma zai rika fita zuwa aiki ne abinsa.