Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Turkiyya: Wani jirgin fasinja ya fado ya rabe uku
Wani jirgin sama ya jirkice a filin jiragen saman Turkiyya inda ya tarwatse tare da raunata mutum 21, a cewar jami'ai.
Rahotanni sun ce jirgin yana dauke da fasinjoji 171 da ma'aikatan jirgin shida lokacin da ya fado a filin jirgin saman Sabiha Gokcen a Santanbul.
Ministan sufuri Mehmet Cahit Turhan ya ce ba a samu asarar rai ba.
Gwamnan Santanbul Ali Yerlikaya ya ce an garzaya da mutum 21 asibiti sannan ana ci gaba da kwashe mutanen da abin ya rutsa da su.
Jirgin na Pegasus Airlines ya sauka ne cikin mamakon ruwan sama bayan ya tashi daga lardin Izmir kamar yadda kafafen yada labaran Turkiyya suka rawaito.
Jami'ai kuma na ci gaba da kokarin zakulo wadanda suka makale cikin jirgin.
Hoton bidiyo da ke watsuwa a shafukan sada zumunta ya nuna wuta ta tashi a jirgin saman sai dai daga bisani masu kashe gobara sun kashe wutar.