Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kama jakadan Birtaniya a Iran
An kama jakadan Birtaniya a birnin Tehran, a daidai lokacin da 'yan kasar ke zanga-zanga bayan gwamnati ta amince da harbo jirgin Ukraine bisa kuskure.
An dai tsare Rob Macaire tsahon sa'a uku, a matakin da Birtaniya ta kira yiwa dokokin kasa da kasa hawan kawara.
Rahotanni sun bayyana cewa Mista Macaire na wajen addu'o'i ga wadanda suka mutu a lokacin da aka harbo jirgin, inda daga bisani wurin zaman makokin ya koma na zanga-zanga.
An cafke shi ne a lokacin da ya ke kan hanyar komawa ofishin jakadancin Birtaniya a birnin Tehran.
Tun da fari Firai Ministan Iran ya ce wannan mataki mafari ne, kuma za a gudanar da bincike dan gano musabbabin hadarin jirgin.
A yanzu dai Iran ta amince sojinta sun harbo jirgin Ukraine mai lamba ne PS752 bisa kuskure, wanda ya ke dauke da fasinja da ma'aikata 179 kuma baki daya sun mutu.
Jaridar Etemad ta Iran, ta wallafa hotunan jakadan a shafin Twitter, jim kadan bayan kafar yada labaran gwamnatin kasar Tasnim ta sanar da kama shi.
Sanarwar da sakataren harkokin wajen Birtaniya Dominic Raab ya fitar, ta ce ''kama jakadanmu a birnin Tehran ba tare da karin bayani kan laifin da aka ce ya aikata ba, ya sabawa dokokin kasa da kasa. A yanzu gwamnatin Iran na kokarin shige gona da iri, Birtaniya ba za ta amince da hakan ba.''