Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An rage wa Trump karfin ikon abka wa Iran da yaki
Majalisar wakilan Amurka ta amince da gagarumin rinjaye kan wani kuduri da ya rage wa Shugaba Donald Trump karfin ikon da zai ba shi damar abka wa Iran da yaki.
Kudurin ya samu amincewar majalisar wakilai da rinjayen kuri'u 30, to amma zai iya fuskantar tirjiya idan ya tsallaka majalisar dattawa da jam'iyyar Republican ke da rinjaye.
Yanzu dole ne Shugaban ya samu amincewar majalisa kafin daukar duk wani matakin soji kan Iran. Sai idan an shiga wani yanayi da aka kai wa Amurka hari.
Kawo yanzu tsakanin Iran da Amurka babu wanda ya sanar da matakin soji na gaba da zai dauka kan rikicin da ke faruwa tsakaninsu.
A wannan makon ne Iran ta kai harin ramuwar gayya kan sansanonin Amurka da ke Iraki, bayan kisan babban kwamandanta Janar Qassem Soleimani da Amurkar ta yi.
Daga yanzu dokar ta hana Shugaba Trump amfani da sojojin Amurka wurin yakar Iran ba tare da amincewar majalisa ba.
Sai dai duk da haka Dokar ta ba shi umarnin kai hari ba tare da neman izini ba, matsawar akwai kwakkwarar hujjar da ke nuna cewa akwai bukatar kare kasar ga harin da aka shirya kai mata.
Haka ma dokar ba ta bukatar sa hannun Shugaban kasa kafin ta fara aiki.
A ranar Alhamis ne Shugabar majalisar wakilan Nancy Pelosi ta sanar da cewa b ata yadda da cewa Amurka za ta zauna lafiya ba bayan da Amurka ta kaddamar da harin jirgi marar matuki kan Janar Soleimani na Iran.
Mista Trump, wanda dan jam'iyyar Republican ne, ya wallafa a Twitter cewa yana fatan " 'yan Republican za su kada kuri'ar kin amincewa da kudirin yaki na Nancy Pelosi".
Ya kuma ci gaba da kare matakin kisan Qasem Soleimani.