Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
An kashe sojin Amurka uku a Kenya
Wani hari da mayakan kungiyar al-Shabaab suka kai sansanin soji da ke garin Lamu a kudu maso gabashin kasar Kenya ya hallaka sojin Amurka uku.
Rundunar sojin Amurka a Afirka ta tabbatar da mutuwar sojojin da jikkatar wasu guda biyu.
Ko a ranar Lahadi kungiyar mai alaka da al-Qa'eeda ta kai wani harin na daban, sai dai kawo yanzu babu wani Karin bayani da hukumomin Kenya suka fitar kan ko akwai sojojin kasar a cikin wadanda suka mutu ko jin rauni ba.
Kwamandan sojin Amurka a Afirkar ya ce soja guda ya mutu da wasu ma'aikatansu biyu a mummunan harin da mayakan kungiyar al-Shabaab suka kai sansanin.
Tuni al-Shabaab mai mazauni a kasar Somalia ta fitar da sanarwa a ciki ta yi ikirarin kai harin tare da cewa sojin Amurka 17 ta hallaka da ma Kenya tara.
Wannan gagarumar nasara ce da kungiyar ta yi a shekaru 13 da suka yi su na kaddamar da hare-hare a kasar Somalia da makwabtanta.
Ana ganin wannan hari zai janyo kakkausar suka daga Amurka da kawayenta.
Ba kasafai dai tsautsayi ke fada wa kan sojin Amurka da ke kasar ba, tun a shekarar 2017 ne sojin Amurkar guda ya mutu a harin da al-Shabaab ta kai a kasar Somalia.
Rundunar sojin Amurka da ke Kenya ta ce an yi musayar wuta tsakaninsu da mayakan Al-Shabaab, lamarin da ya janyo jiragen farar hula shida suka lalace.
Tun da fari ma'aikatar tsaron Kenya ta rawaito an gano gawar mayaka shida a inda akai musayar wuta tsakaninsu da sojoji.