Zakarun Turai: Messi ne kawai ya fi Salah

Mohamed Salah lokacin da za ya ci Salzburg

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A karon farko Mohamed Salah ya ci bal da kafar dama daga wajen da'ira tun da ya bar Masar ya koma Turai da wasa
An wallafa

Zakarun Turai, Liverpool, sun kai matakin gaba na kungiyoyi 16 a gasar cin Kofin Turai, bayan da suka zama na daya a rukuninsu na biyar (Group E), bayan doke Red Bull Salzburg 2-0.

Liverpool din wadda take bukatar akalla maki daya ta kai matakin na sili-daya-kwale, da farkon wasan a karawar ta Talatar nan da suka yi a gidan Salzburg din, masu masaukin sun rika kai musu hare-hare masu hadari.

Sai dai Zakarun sun karya lagon masu masaukin nasu, lokacin da Naby Keita ya daga raga da ka, a minti 57 da wata bal da Sadio Mane ya aika masa.

Bayan dakika 100 da cin kwallon farkon sai kuma Mohamed Salah ya zura ta biyu, da wani kwyakkyawan ci na kusurwa.

Kungiyar Premier ta kociya Jurgen Klopp tana bukatar maki uku ne ta zama ta daya a rukunin nasu saboda Napoli da ke bi mata baya ta doke Genk 4-0, a daya karawar rukunin da aka yi a gidan Napoli.

A ranar Litinin Liverpool za ta san kungiyar da za a hada ta da ita, a zagayen gasar na gaba na kungiyoyi 16, bayan fitar da jadawalin da za a yi a birnin Nyon, na Switzerland da karfe 12:00 na rana agogon Najeriya. Za a iya hada ta da kungiyoyin Sifaniya, Real Madrid ko Atletico.

Sadio Mane lokacin da ya yanke golan Salzburg

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Sai da Sadio Mane ya yanke golan Salzburg ya ba wa Naby Keita ya ci ta farko

A yanzu Salzburg, wadda ta ci kwallo 87 a wasa 24 kafin wannan karawa, ta fadi daga gasar ta Turai ta Champions League, amma ta yi nasarar shiga matakin kungiyoyi 32 na gasar Turai ta Europa.

Bayan kwallon da ya ci a wasan, a yanzu Mohamed Salah ya taka rawa a kwallo 27 ta gasar kofin na Turai da Liverpool ta zura, inda ya ci 19 kuma ya bayar aka ci 8.

Da wannan bajinta a yanzu Messi ne kadai ya fi Salah taka irin wannan rawa ta zura kwallo a gasar ta Turai, ta Champions League, tun bayan da ya koma Liverpool a 2017, inda Messi yake da 28.

Wane Wasa Liverpool za ta yi a nan gaba kuma?

Yanzu kungiyar za ta mayar da hankalinta ne wajen kokarin cin kofinta na gasar Premier na farko.

A ranar Asabar za ta karbi bakuncin Watford a wasan da za su yi da karfe 1:30 na rana agogon Najeriya, inda za ta yi fatan ci gaba da zama jagora ko ma ta kara tazarar da ta bayar a gasar.