Leonardo Bonucci: Dan wasan Juventus ya sabunta kwantaraginsa

An wallafa

Dan wasan Italiya Leonardo Bonucci ya sanya hannu kan karin kwantaragin shekara daya a Juventus.

Yanzu haka dai dan wasan zai ci gaba da kasancewa a Juve har zuwa shekarar 2024.

Dan wasan, mai shekara 32, ya buga wa kungiyar Serie A wasanni 376, bayan ya koma kungiyar a shekarar 2010.

Ya koma AC Milan a shekara ta 2017, amma ya sake komawa Juventus din bayan shekara guda da barinta.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce "wannan labari ne mai dadi; wanda ke cewa Leonardo Bonucci zai ci gba da kasancewa a Juventus din na tsawon lokaci."

Bonucci yana taka leda sosai a kowanne wasa da kungiyar ta yi.

Juventus dai yanzu haka ita ke saman teburin Serie A, maki daya tsakaninta da Inter Milan wadda ke mataki na biyu.

Dan wasan, ya lashe kofuna 14 tare da Juventus tun lokacin da ya koma can daga Bari shekara tara da ta gabata, ciki har da kambun Scudetto guda bakwai.