Yawancin gidaje a Tanzania ba su da masai

An wallafa

Wani rahoto da aka fitar a Ranar Bandaki ta Duniya, ya gano sama da kashi 90 na gidajen babban birnin kasar Tanzania ba su da masai.

Rahoton ya ce kusan gidaje miliyan hudu a birnin Dar es Salaam sun dogara ga masu kwashe bahaya ba bisa ka'ida ba su kwashe na gidajensu.

Ko kun san 19 ga watan Nuwamba ne ranar Bandaki ta Duniya?

A wannan shekarar za a mayar da hankali ne kan kiwon lafiya, kariya da martaba. Da halin da duba gari ko 'yan Tula da ke aiki a wurare masu hadari da rashin tsafta ke samun kansu a ciki.

Wadanne kalubale suke fuskanta, kuma ta yaya za a taimaka musu? Kamar yadda daya daga cikin masu kwashe bahayar ya yi korafi.

Yawancin wadanda ke wannan aikin maza ne da suke aiki da tsakar dare wadanda sana'arsu ita ce kwashe dattin da jama'ar birnin ke fitarwa.

Rahoton halin da suke shiga na hadin gwiwa ne tsakanin kungiyar kwadago ta duniya da Bankin Duniya da kungiyar WaterAid.

'Yan Tula na shiga cikin salga, ko matattarar bahaya dauke da bokitai da shebur don kwashe bahayar, a wasu lokutan kuma suna amfani da hannayensu.

Babu wata kariya da suke amfani da ita kamar safar hannu wanda, don gujewa fadawa hadarin kamuwa da cututtuka, a wasu lokutan ma har da mutuwa.

Babu wata kididdiga da ta nuna yawan 'yan Tula da suka kamu da cuta ko fadawa wani hadari saboda baki dayan aikin nasu ba bisa ka'ada suke yi ba.

Kungiyoyi kamar WaterAid na aiki tare da masu kwasar bahayar don taimaka musu gudanar da sana'ar ta hanyar da ta dace, inda gwamnati za ta san da zamansu da ba su kariya idan bukatar hakan ta taso.

A bangare guda gwamnatin Tanzania ta bayyana hadarin da ake fuskanta na ruftawar salga da irin cututtukan da ke yaduwa ta dalilin hakan musamman a unguwannin marasa galihu.

Sai dai ga yawancin mazauna unguwannin birnin Dar es Salaam, sun gwammace su kira 'yan Tula ta bayan fage don kwashe bahaya da dan kudi kalilan, maimakon kiran na gwamnati da suke cajin kudin mai yawa.