Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Evo Morales: Ba na fargabar komawa Bolivia
An wallafa
Tsohon shugaban Bolivia Evo Morales ya ce ba ya fargabar dawowa kasarsa domin yin takara a zabe mai zuwa, matsawar jam'iyyarsa ta aminta ta tsayar da shi takara.
Rahotanni sun ce a kalla mutum biyar sun mutu bayan wani rikici tsakanin jami'an tsaro da kuma magoya bayan Mista Morales.
Sai dai rikicin ya fi shafar garin Cochabamba inda Mista Morales ya ke da goyon baya sosai.
Da yake jawabi daga birnin Mexico inda yake gudun hijira, tsohon shugaban da aka tursasawa barin gado, ya ce a shirye yake ya koma gida domin shiga zabe, duk da barazanar tsare shi da a ka yi.