Liverpool na neman Jadon Sancho, Pep zai koma Bayern?

An wallafa

Akwai yiwuwar Liverpool za ta sayi dan wasan gaban kungiyar Borussia Dortmund Jadon Sancho mai shekara 19. (Mail)

Tottenham na fuskantar babban kalubale, bayan da 'yan wasanta Christian Eriksen da Danny Rose da Toby Alderweireld da kuma Jan Vertoghen suka bayyana aniyarsu ta barin kungiyar da zarar yarjejeniyarsu ta kare. (Star)

Ga alama mai horar da kungiyar Manchester City Pep Guardiola ba ya jin dadin zamansa a Ingila, kuma ana ci gaba da hasashen cewa zai koma kungiyarsa ta da wato Bayern Munich (Bild - a Jamusanci)

Kungiyoyin Juventus da Barcelona na neman dan wasan tsakiyar Chelsea, Willian, wanda yarjejeniyarsa ke dab da karewa. (Mirror)

A wata mai kama da haka mai horar da 'yan wasan Inter Milan Antonio Conte na sha'awar sayen dan wasan gaban Chelsea Olivier Giroud wanda yarjejeniyarsa za ta kare badi. (Gazzetta dello Sport, daga Express)

Mai horar da 'yan kwallon Netherlands Ronald Koeman ya ce akwai yiwuwar ya karbi horar da Barcelona da zarar an dawo gasar kasashen nahiyar Turai ta 2020. (Mirror)

Akwai yiwuwar Napoli ta sallama wa Manchester United mai tsaron bayanta dan kasar Senegal Kalidou Koulibaly wanda Arsenal ke kan nema. (Ilmattino - ta Italiyanci)

Manchester City ta rubuta wa shugaban masu busa wasannin Ingila Mike Riley takardar nuna damuwa kan yadda na'urar da ke tantance abinda ya faru a wasa wato VAR ke aiki.

Hakan ya biyo bayan rashin nasarar da kungiyar ta yi a hannun Liverpool, wasan da aka samu takaddama kan hukuncin na'urar. (Times)