Qatar za ta soke tsarin aiki na Kafala

An wallafa

Qatar na shirin soke dadaddiyar tsarin nan da ke bukatar ma'aikata 'yan kasashen waje su mika 'yancinsu ga wanda ya dauke su aiki a kasar.

Tsarin mai suna Kafala ya yi kama da bauta, kuma Qatar na shan kakkausar suka daga kasashen waje.

Kasar na tsakiyar wasu manyan ayyukan raya kasa, musamman ma na karban bakuncin gasar kwallon kafa ta duniya da za ta dauki nauyi a 2022.

Tsarin mai suna Kafala na daure ma'aikata 'yan kasashen waje da 'yan Qatar da suka fara daukarsu aiki.

Ma'aikatan da ke ayyuka kamar na gine-gine ba sa iya barin kasar sai wanda ya dauke su ya ba su izini.

Sannan ma'aikatan ba sa iya sauya wurin aiki - ko da kuwa ana gallaza musu ne - sai mai gidan nasu ya amince.

A 'yan watannin baya, Qatar ta yi sassauci ga tsarin bayar da izinin ficewar, amma yanzu tana son kawar da tsarin na Kafala gaba daya.

Ana kuma sa ran samar da mafi kankancin albashi ga kananan ma'aikata da tsarin na Kafala ya shafa.

Wadannan sauye-sauye ne masu muhimmanci ba ga Qatar kawai ba, har ma ga sauran kasashen yankin kamar Hadaddiyar Daular Larabawa da Kuwait.

Wadannan kasashen ma na gudanar da irin wannan tsari na Kafala mai mayar da ma'aikata 'yan kasashen ketare tamkar bayi.