Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zidane: Idan mun yi nasara a yabe ni idan mun fadi a soke ni
Yayin da Real Madrid ke shirye-shiryen karawa da Osasuna a La Liga wasan mako na 6, Zinedin Zidane ya amsa tambayoyi kan halin da tawagar tasa take ciki da kuma zamnsa a Madrid din.
Kungiyar tana kokarin dorawa ne kan nasarar da ta samu a Sevilla a ranar Lahadi, kuma Zidane ya ce "idan muka samu nasara a yabe ni idan kuma aka ci mu a soke ni".
Zidane yana wannan magana ne a taron manema labarai gabanin wasan da Madrid za ta karbi bakuncin Osasuna a ranar Laraba.
"Abin ba ya damuna, haka yake kullum. Wajibi ne mu mayar da hankalinmu kan wasanni kuma abin da nake yi kenan," in ji Zidane.
Yanzu haka Barcelona tana mataki na takwas a teburi bayan rashin nasara a hannun Granada ranar Asabar, sai dai kocin Madrid din kauuce wa magana kan halin da abokan hamayyarsu ke ciki.
"Abin da ke faruwa yanzu da Barcelona zai iya faruwa da Atletico Madrid. Abin da ya kamata mu yi shi ne, mu yi bakin kokarinmu wajen cin maki mai yawa.
"Mu saka dukkanin kwarewarmu a cikin fili kuma 'yan wasana su ne mafiya kwarewa."
Wasannin Real Madrid biyar na gaba:
Laraba 25 ga Satumba: Real Madrid 8:00 Osasuna - La Liga
Asabar 28 ga Oktoba: Atletico 8:00 Real Madrid - La Liga
Talata 1 ga Oktoba: Real Madrid 5:55 Club Bruges - Champions League
Asabar 5 ga Oktoba: Real Madrid 3:00 Granada - La Liga
Asabar 19 ga Oktoba: Mallorca 20:00 Real Madrid - La Liga