Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Bincike: Maleriya na ci gaba da bijire wa magunguna
Wani sabon rahoton masanan kimiyya ya ce aikin takaita yaduwar cutar zazzabin cizon sauro na cikin hatsari daga bijire wa magunguna barkatai da kwayar cutar ke yi.
Nazarin wanda ya bi diddigin kwayoyin cutukan da ke yada maleriya a Afirka ya gano siffofin kwayar halittar gado na kwayar cutar Plasmodium falciparum a yankuna daban-daban na Afirka.
Wannan ya hadar da sabubban gado da ke sanya kwayar cutar bijirewa magunguna birjik na yaki da maleriya.
Binciken ya yi karin haske kan yadda ake ta samun bijire wa magungunan cutar cizon sauro a yankuna daban-daban da kuma yadda halayyar bijirewar take matsa wa a fadin Afirka, lamarin da masana suka ce ya sanya ci gaban da aka samu a baya cikin hatsari.
Cutar maleriya, matsala ce da ta addabi duniya, kuma nau'o'in kwayar cutar ta Plasmodium falciparum na bazuwa a yankin Kudu da sahara. A tsakanin shekara ta 2000 zuwa 2015, yunkurin kawar da cutar ya yi nasarar ganin raguwar mace-macen zazzabin cizon sauro a fadin duniya daga mutum dubu 864 zuwa dubu 429 a shekara.
A shekara ta 2015, kashi 92 cikin 100 na mace-macen da aka samu saboda maleriya a duniya sun faru ne a Afirka, kuma kashi 74 cikin 100 na mamatan kananan yara ne 'yan shekara biyar ne ko k'asa da haka. Sai dai wannan bincike da aka wallafa a Mujallar Science journal ya ce matukar ba a kirkiro wasu sabbin hanyoyin magance cutar zazzabin cizon sauro ba, ci gaban da aka samu na iya shiga cikin hatsari.
Binciken ya zo ne daga wata gamayyar masanan kimiyya 'yan Afirka ta farko da ke aiki kan ire-iren kwayar cutar Plasmodium a Afirka.
Sun dai nazarci ire-iren kwayar halittar gadon wannan kwayar cuta ta Plasmodium wadda ta zama ja'iba a kasashe da dama cikin yankin kudu da sahara da suka hada da Habasha da Ghana.
Nazarin ya gano cewa kwayar cutar ta sha banban a halittun gadonta da wata 'yar'uwarta da ke wani yanki daban na Afirka. Farfesa Abdoulaye Djimde, na Cibiyar Wellcome Sanger, ya ce: "sabanin bincike-binciken da suka gabata, sun gano nau'in kwayar cutar a yammaci daban, da nau'in tsakiya sai kuma irin ta yankin gabashi ita daban, ga kuma ta Habasha mai matukar sassauya siffofi.