Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Labaran da aka fi karantawa a shafin BBC Hausa a 2018
Mun duba alkalumman mu tun daga ranar 1 ga watan Janairu har zuwa 31 ga watan Disambar shekarar 2018 inda muka gano labarai 10 da aka fi karantawa a gaba daya shekarar.
Za ku yi mamakin cewa labarin sako 'yan matan Dapchi dai ba ya cikin jerin.
Kuma labaran siyasa ne dai suka mamaye jerin.
1) Ko Buhari bai isa ya hana ni fadar gaskiya ba - Dino
Masu ziyartar shafinmu sun so wannan labarin sosai inda dan majalisar dattawan Najeriya mai jawo ce-ce-ku-ce, Sanata Dino Melaye ya ce ba zai yi shiru da bakinsa ba matukar ya ga wani abu da ake gudanarwa a gwamnati da bai dace ba.
''Ni ba na tsoron kowa, idan akai abin da ba daidai ba kuma na ga babu gaskiya a ciki sai na fada, ba na jin tsoron kowa indai ina da gaskiya."
"A halin da ake ciki ni fa ko Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ko Bukola Saraki, ko Dogara kai ko uban da ya haife ni idan ya yi ba daidai ba sai na fada, babu wanda ya isa ya hana ni fadar gaskiya sai dai a kashe ni,'' inji Dino Melaye.
2) Su waye za su ja da Buhari a zaben 2019?
Labarin da ya zo na biyu a jerin wani labari ne da Umar Rayyan ya yi nazari kan manyan 'yan siyasar najeriya da ke da muradin tsayawa takarar shugabancin kasar tare da shugaba mai ci Muhammadu Buhari.
'Yan siyasar dai sun hada da Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawan kasar da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Alhaji Atiku abubakar da Alhaji Sule Lamido da Ayodele Fayose.
3) An 'kashe Buharin Dajin da ya addabi Zamfara'
Wannan labarin ne a kan kama Buharin Daji jagoran barayin shanu da suka addabi jihar da hare-hare, kuma shi ne na uku da aka fi karantawa a shafin.
An kama Buhari Tsoho, wanda aka fi sani da Genaral Buharin Daji a wani farmaki da aka kai masa da taimakon wasu abokan fashinsa da suka raba gari.
4) Saraki ko Kwankwaso: Wa zai iya ja da Buhari a APC?
Masu iya magana kan ce "sawun giwa ya take na rakumi" a duk lokacin da suka yi kokarin kwatanta karfin wani abu ko mutum kan abokan karawarsa, da kuma nuna yadda ya yi musu fintinkau ko kuma zai iya share su ya wuce ba tare da wata matsala ba.
Naziru Mika'ilu ya yi nazari kan wanda zai iya yin galaba wajen tsayawa takara da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a zaben 2019.
Bisa alama masu ziyartar shafinmu sun ji dadin wannan nazari domin kuwa shi ne na hudu a jerin labarai 10 da aka fi karantawa a shafinmu.
5) Yadda Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai
Babu shakka ma'abota BBC Hausa na son labaran wasanni, shi yasa a watan Mayu da muka wallafa labarin yadda kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta lashe kofin Zakarun Turai kai tsaye, aka samu masu ziyarta shafin sosai.
Wannan labari da muka yi kai tsaye dai shi ne ya zo na biyar a wadanda aka fi karantawa.
6) 'Sayyadina Umar ya taba aika sako Daular Borno'
Tarihi na da matukar muhimmanci a rayuwa ganin cewa yana wayar da kai, kara ilimi da fahimta kan wasu al'amura da ba a sani ba.
Wannan makala da Awwal Janyau ya rubuta kan Daular Barno ta yi tasiri sosai ga makaranta wannan shafi.
An duba tarihin Daular Borno ta hanyar tattaunawa da Masana tarihi Alhaji Zanna Hassan Boguma daraktan da ke kula da al'amuran masarautu a Borno, da Farfesa Adam Muhammad Ajiri na sashen nazarin addinin Islama a Jami'ar Maiduguri, wadanda kuma suka yi kokarin amsa wasu tambayoyi da masu saurare suka aiko.
Shi ne labari na shida da aka fi karantawa.
7) Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya yau
Wannan labari ne kai tsaye kan abubuwan da suka faru a kasashen Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru da Chad.
Shafin ya duba labarin cikar Shugaba Buhari shekara uku da lashe zabe da kuma yadda babban taron jam'iyyar APC da wata zanga-zangar adawa da 'yan Ghana suka yi da dai sauran su.
8) 'Yan sanda sun kama Aisha Buhari ta bogi
Rundunar 'yan sandan Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun kama wata mata da ke yin sojan-gona a mastayin mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari.
Wata sanarwa da kakakin rundunar DSP Anjuguri Manzah ya aikewa manema labarai ta ce an kama matar, mai shekara 37 'yar asalin jihar Filato ne a birnin.
"Bayan an kama ta ne sai aka gano wata wayar tarho mai dauke da layin da aka yi wa rijista da sunan Aisha Buhari, mai dakin shugaban Najeriya.
An ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ta damfara, sannan za a mika ta a gaban kotu da zarar an gama bincike", in ji sanarwar.
9) Hatsaniya ta kaure a zaben fidda gwani
A watan Satumba ne aka yi zabukan fitar da gwamni a jam'iyyun siyasar Najeriya.
Shafin ne da ya kawo labarai da sharhi kai tsaye game da yadda ake zaben fidda gwani a mafi yawan jihohin Najeriya.
10) Tsoffin 'yan sabuwar PDP sun gana kan Buhari
Ga alama labaran siyasa ma dai na da farin jini don kuwa ma'abota wannan shafi sun mayar da hankali kan labaran da suka danganci siyasa.
Wannan labarin yadda tsoffin 'yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, su ka yi taro kan makomarsu a jam'iyyar APC.
Wadannan su ne labarai 10 da ak fi karantawa cikin dubban labaran da muka wallafa muku a shekarar 2018.
An karanta su sau dubun-dubata, kazalika wadanda suka biyo bayansu ma an karanta su ba adadi.
Muna fatan mu kawo muku labaran da suka fi wadannan dadi da armashi da ilimantarwa a shekarar 2019.