Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Leah Sharibu na neman Buhari ya taimake ta
Yarinyar nan daya tilo da ta rage a hannun 'yan Boko Haram da aka sace daga makarantar sakandaren Gwamnati a Dapchi Leah Sharibu ta roki Shugaba Muhammadu Buhari ya kai mata dauki.
"Ina kuka wa gwamnati da kuma jama'a ku taimake ni ku fidda ni daga cikin wannan yanayi da nake ciki" in ji Leah, a wani sakon murya da jaridar TheCable da ake bugawa a intenet ta wallafa.
Wannan shi ne karo na farko da aka ji duriyar Leah tun bayan aka sace su da 'yan uwanta da 'yan Boko Haram suka yi a makarantar sakandaren kwana ta garin Dapchi a jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Daga baya 'yan Boko Haram din sun sako duka 'yan matan 110, in banda Leah, da suka ki sako ta saboda "ta ki barin addinin Kiristanci," a cewar sauran 'yan matan.
Biyar daga 'yan matan da aka sace dai sun mutu a hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka sace su a watan Fabrairun bana.
Bangaren da suka yi mubaya'a ga kungiyar IS wanda ke karkashin Abu Mus'ab Al-barnawani ne suke rike da Leah.
A cikin sakon muryar, Leah ta nemi jama'a su ji tausayinta da iyayenta, da 'yan uwanta a fitar da ita daga "halin da ta ke ciki".
Wani hoto da kafar larabaran ta buga ya nuna Leah na zaune a kan tabarma sanye da hijabi.
Majiyar TheCable ta ce hoton da kuma muryar wata shaida ce ta cewa Leah tana raye, wanda hakan tamkar wani mataki ne a yunkurin tattaunawa da gwamnati take yi da Boko Haram domin sakin dalibar.
Majiyar ta shaida wa TheCable cewa, tun farko kungiyar IS ce ta sa aka sako sauran 'yan matan, inda majiyar ta ce shugabannin kungiyar na duniya sun ga baiken Boko Haram kan sace 'yan mata Musulmi.
Kuma a cewarta hakan ce ta sa aka sako 'yan matan 110 ranar 21 ga watan Maris din bana, in ban da Leah wacce ita kadai ce musulma a cikin 'yan matan.
Gwamnatin Najeriya dai ta dage cewa ba a biya ko sisin kwabo ba kafin sako 'yan matan.
To sai dai a baya-bayannan wani rahoton wani kwamitin Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa sai da aka biya makudan kudade gabanin sakin 'yan matan, rahoton da gwamnatin Najeriya ta musanta.
- A ranar 19 ga Fabrairu aka sace 'yan matan
- Dalibai 110 aka sace a makarantar Dapchi
- An sace su kwana daya bayan sojoji sun fice
- An shiga rudani kan sace 'yan matan
- Da farko an ce 'yan matan sun shiga daji ne domin buya
- Sai da aka dauki tsawon mako daya kafin gwamnati ta amince an sace su
- Gwamnatin Yobe ta yi ikirarin ceto 'yan matan, kafin daga baya ta nemi afuwa
- Bangaren Abu Musab al-Barnawi ne ake tunanin sun sace 'yan matan
- Boko Haram ba ta fito ta yi ikirarin sace 'yan matan ba
- Sace 'yan Matan Dapchi ya tuna wa duniya da 'yan matan Chibok
- Wannan ya nuna har yanzu Boko Haram barazana ce
- Sun gana da Shugaba Buhari