Matasan 'yan wasan da za su 'haskaka' a Rasha 2018

Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mbappe na cikin matasan da ake ganin nan gaba za su iya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya
An wallafa

Gasar cin kofin duniya fage ne na tamaular duniya da matasan 'yan kwallo ke nuna kansu.

Duk da cewa gasar ta kunshi zaratan 'yan kwallon duniya irin su Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da ganiyarsu ke dab da kawo wa karshe, haka ma gasar ta kunshi matasan da ake ganin za su gaji manyan 'yan wasan.

Wannan ne karon farko da yawancin matasan za su buga gasar cin kofin duniya, kuma gasar kamar kasuwar baje-koli ce ta matasan 'yan kwallo.

BBC ta zabo wasu matasan 'yan wasa bakwai da ake ganin za su taka rawar gani a gasar.

Marcus Rashford - Ingila

Rashford

Asalin hoton, Reuters

Rashford dan shekara 20, ana kallonsa a matsayin wani babban arziki ga tawagar Ingila a Rasha.

Rashford ya buga wasan sada zumunci da Ingila ta doke Najeriya, kuma saura kiris dan wasan ya jefa kwallo a raga.

Dan wasan na cikin matasan da ake ganin za su taka rawar gani a Rasha musamman idan ya samu dama ana sako shi akai-akai.

Kylian Mbappe - Faransa

Mbappe

Asalin hoton, Getty Images

Mbappe mai shekara 19 na cikin matasan da za a kalla a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Dan wasan na Faransa ya taimakawa PSG lashe kofin Lig 1 a kakar da aka kammala, kuma ya ja hankalin duniya bayan ya taimakawa Monaco lashe kofin Lig 1 kafin ya koma PSG a 2017.

Mbappe na cikin matasan da ake ganin nan gaba za su iya lashe kyautar gwarzon dan wasan duniya.

Frederico Rodrigues da aka fi sani da Fred - Brazil

Fred

Asalin hoton, AFP

Kwanan nan Manchester United ta kammala cinikin Fred dan wasan Brazil mai shekara 25 daga Shakhtar Donestk a kan fam miliyan 47.

Ana ganin dan wasan zai yi amfani da gasar cin kofin duniya domin nuna kansa.

Wannan ne karon farko da zai wakilci Brazil a gasar.

Ousmane Dembele - Faransa

Dembele

Asalin hoton, AFP

Dembele mai shekara 21 wanda Barcelona ta saya a kan sama da fan miliyan 100, yana cikin matasan da za su ja hankali a Rasha.

Duk da dan wasan ya fuskanci kalubale a kakarsa ta farko a Barcelona saboda raunin da ya shafe watanni yana jinya, amma dama ce da zai nuna wa duniya darajarsa.

Dembele gwanin yanka ne da zarafin cin kwallo a raga. Barcelona ta sayo shi ne daga Borusssia Dortmund domin maye gurbin Neymar.

Wilfred Ndidi - Najeriya

Ndidi

Asalin hoton, Getty Images

Dan wasan tsakiyar na Najeriya na cikin 'yan wasan da ake ganin za su kayatar a gasar cin kofin duniya a Rasha.

Ndidi da ke taka leda a Liecester City, ana ganin zai taka rawar gani a Rasha, musamman yadda yake rike tsakiyar fili da kuma yunkurin kai hari.

Kungiyoyi da dama za su zuba ido su ga irin rawar da zai taka a gasar.

Gabriel Jesus - Brazil

Gabriel Jesus in action during the international soccer friendly match between Brazil and Croatia at Anfield in Liverpool,

Asalin hoton, EPA

Jesus mai shekara 21 yana cikin matasan da ke kan ganiyarsu a duniyar tamaula. Kuma wannan ne karon farko da zai buga gasar cin kofin duniya.

Dan wasan ya taimakawa Manchester City lashe kofin Firimiya a kakar da aka kammala.

Ana ganin rawar ganin da Brazil za ta taka a gasar zai ba Jesus damar lashe kyautar gwarzon matashin dan wasan a Rasha.

Marco Asensio - Spain

Asensio

Asalin hoton, Getty Images

Asensio mai shekara 22 yana cikin tawagar Real Madrid da suka lashe kofin zakarun Turai sau uku a jere.

Spain ta tafi da matashin dan wasan maimakon wadanda aka saba gani irinsu Fabregas da Morata da kuma Juan Mata saboda yadda yake murza-leda da kuma cin kwallaye.

Asensio ya ci wa Real Madrid kwallo 10 a kakar da aka kammala.