Yadda Martin Luther King ya kwatowa bakake 'yanci a Amurka

An wallafa

Ana bikin tunawa da shekaru 50 da mutuwar Martin Luther King Jnr. wanda yayi fafutukar Civil Rights Movement domin nemawa bakake 'yanci a Amurka tun shekarun 1950.

Kisan gillar da aka yi wa Martin Luther King Jr ya girgiza manyan biranen Amurka inda tarzoma ta barke a biranen Washington da Chicago da Baltimore da Kansas City da kuma Missouri.

An haife shi a 15 ga watan Janairun 1929 zuwa 4 ga watan Afrilun 1968.

Dr King wani Ba'amirken fasto ne na cocin Baftis kuma mai fafutukar yaki da nuna bambancin launin fata a Amurka.

An ba Dr King lambar yabo ta Nobel a watan Oktobar 1964 domin fafutukr samar da zaman lafiya da ya yi.

Kuma a 1965 yana cikin wadanda suka shirya wani gagarumin maci daga birnin Selma zuwa Montgomery.

Amma a lokacin da ake bikin cika shekara 50 da mutuwarsa, ana ganin ya kamata a sake duba sauyin da sakonsa ya kawo a Amurka.

Ya yaki wariyar launin fata a Arewacin Amurka, ba a kudancin kasar kawai ba. Ya kuma rika matsa wa gwamnati ta dauki matakan kawar da talauci da rashin daidaito wajen albashi tsakanin bakaken fata da turawa.

Ya kuma nemi a daina yake-yake domin suna karkatar da kudaden gina kasar.

Sai a shekarar 1983 ne tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan ya sanya hannu a kan dokar da ta ware wata rana ta musamman domin karrama Dr King.