Real Madrid ta yi bikin lashe Champions League na 14

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

An wallafa

Magoya bayan Real Madrid da yawa ne suka yi bikin lashe Champions League na 14 a dandalin Plaza de Cibeles.

Ranar Asabar Real Madrid ta yi nasara a kan Liverpool da ci 1-0 a wasan karshe da ya bai wa kungiyar Sifaniya damar lashe babbar gasar tamaula ta zakarun Turai karo na 14 jumulla.

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

Magoya bayan Real Madrid ne suka taru makil a dandalin, don taya kungiyar da 'yan wasa, wannan bajintar da suka yi, inda aka yi bikin a dandalin Cibeles, bayan da suka zagaya birnin.

An kafa kyalle da yawa masu dauke da sakon farinciki da alfahari da taya Real Madrid murnar daukar La Liga da Champions League a kakar nan.

Real Madrid

Asalin hoton, Real Madrid FC

Real ce ta dauki na La Liga na bana, kuma na 35 jumulla, kofin da ba wata a Sifaniya da ta kama kafarta a yawan dauka, kamar yadda ta yi zarra a Champions League.

'Yan wasa sun fito kan dandalin da aka tanada, inda suka dunga rawar murna tare da magoya baya.

'Yan wasa sun yaba da rawar da magoya baya suka taka da kungiyar ta kai ga wadan nan nasarorin a kakar nan.

'Yan wasan sun kuma yi alkawarin za su kwazo a kaka mai zuwa don kara faranta ran magoya baya, da ci gaba da daga darajar kungiyar.