'Mauricio Pochettino da Kylian Mbappe za su ci gaba da zama a PSG a badi'

An wallafa

Kociyan Paris St Germain, Mauricio Pochettino ya ce yana da tabbacin zai ci gaba da aiki a badi a kungiyar tare da Kylian Mbappe.

Tun farko makomar Pochettino na tangal-tabgal, bayan da aka yi waje da PSG daga Champions League a zagaye na biyu a bana - kofin da kungiyar ke fatan dauka ruwa a jallo.

An ci gaba da yada cewar kungiyar Faransa za ta sallami dan kasar Argentina, duk da lashe Ligue 1 a bana da ya yi, wanda ya koma PSG a 2021.

Ana ta alakanta Kylian Mbappe da cewar zai koma taka leda a Real Madrid, bayan da kwantiraginsa zai kare a karshen kakar nan a PSG.

''Ina da tabbaci 100 bisa 100 zan ci gaba da aiki a Parc des Prince a kakar badi tare da Mbappe.

''Haka ni dai nake tsammani kamar yadda na sanar da ku a yau, Abin da zan iya sanar da ku kenan, ba wani abun da zan kara a kan maganar. Abin da ni dai nake ji kenan.

"Haka kwallon kafa ta gada, ba wanda zai ce maka ga abin da zai faru nan gaba. Amma zan iya amsa tambaya bisa abin da na sani ko halin da ake ciki. Kuma abin da na yi kenan.''

Haka kuma Pochettino ya sanar cewar yana tattaunawa da mahukuntan kungiyar kan makomarsa ta nan gaba.