Afcon 2021: Masar ta doke Kamaru mai masaukin baƙi a gasar

Asalin hoton, KENZO TRIBOUILLARD
Wasu mazauna Kamaru mai masaukin baƙi a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta Afcon 2021 sun bayyana wa BBC Hausa halin da suka shiga bayan doke tawagar ƙasar da Masar ta yi a wasansu na yammacin Alhamis.
Bayan shafe minti 90 ana gumurzu, babu wanda ya yi nasara. Aalkalin wasa ya kara minti 30, inda a nan ma ba a samu wanda ya yi nasara ba har sai da aka je ga bugun fanareti.
A nan ne Masar ta doke Kamarun da ci 3-1.
Yanzu dai Masar za ta buga wasan ƙarshe da Senegal ranar Lahadi.
Golan Masar, Gabaski, ya yi kokari ta hanyar kaɗe ƙwallo biyu, yayin da daya ta tsallaka saman raga.
Karawar hamayya tsakanin Kamaru da Masar
Wannan ne karo na 11 da kasashen suka kece raini a tsakaninsu a Afcon, wasan da kasashe ke haduwa da juna da yawa a tarihin gasar.
Masar ta yi nasara a wasa hudun da suka yi a baya da rashin nasara a daya da cin kwallo tara. Ta zura kwallo biyu kacal a haduwa bakwai a baya da Indomitable Lions, sannan yin nasara a karawa daya da canjaras biyu da shan kashi a uku.
Kamaru ta kai zagayen gaba a wasa bakwai daga tara da ta yi a daf da karshe a Afcon, Masar ce kan gaba ta yi hakan sau takwas a tarihi.
Mai masaukin baki ta kasa kai wa matakin gaba a wasa uku daga biyar da ta yi a baya a tarihin babban gasar tamaula ta Afirka.
Tun daga farkon gasar 2017 ba wani dan wasa da ya yi sanadin kwallo tara a raga kamar Mohamed Salah a Afcon, wanda ya ci shida ya kuma bayar da uku aka zura a raga.
Sai Kyaftin din Kamaru, Vincent Aboubakar wanda ya ci bakwai ya kuma bayar da biyu aka zura a raga.
A gasar bana Aboubakar ya ci kwallo shida da kuma takwaransa, Karl Toko Ekambi mai biyar a raga a wasannin bana.
A wasa 13 baya da suuka kece raini Masar ta yi nasara a shida da canjaras hudu, Kamaru ta ci uku.
Wasu wasannin 13 da suka fafata a baya:
African Cup of Nations Ranar Lahadi 5 ga watan Fabrairun 2017
- Egypt1 - 2Cameroon
Wasan sada zumunta Lahadi 20 ga watan Mayun 2012
- Egypt2 - 1Cameroon
African Cup of Nations Litinin 25 ga watan Janairun 2010
- Egypt3 - 1Cameroon
African Cup of Nations Asabar 10 ga watan Fabrairun 2008
- Egypt1 - 0Cameroon
African Cup of Nations Talata 22 ga watan Janairun 2008
- Egypt4 - 2Cameroon
Kofin duniya Asabar 8 ga watan Oktoban 2005
- Cameroon1 - 1Egypt
Kofin duniya Sunday 5 ga watan Satumbar 2004
- Egypt3 - 2Cameroon
African Cup of Nations Talata 3 ga watan Fabrairun 2004
- Cameroon0 - 0Egypt
African Cup of Nations Litinin 4 ga watan Fabrairun 2002
- Cameroon1 - 0Egypt
Wasan sada zumunta Litinin 22 ga watan Disambar 1997
- Egypt2 - 0Cameroon
Afirkan Cup of Nations Alhamis 18 ga watan Janairun 1996
- Cameroon2 - 1Egypt
Wasan sada zumunta Laraba 16 ga watan Maris din 1994
- Egypt0 - 0Cameroon
Afirkan Cup of Nations Juma'a 21 ga watan Maris 1986
- Egypt0 - 0Cameroon










