Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Afcon 2021: Ko Nigeria za ta ci Tunisia ta kai quarter finals kuwa?
Najeriya za ta buga wasa da Tunisia a fafatawar zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka a Kamaru da za su kece raini a Garoua ranar Lahadi.
Ranar Alhamis aka tantance tawaga 16 da suka kai gurbin shiga zagaye na biyu a gasar bana, inda za a fara karawa tsakanin Burkina Faso da Gabon a Limbe a wasan farko na zagaye na biyu ranar Lahadin.
Wasa na biyu a zagayen kungiyoyi 16 tsakanin Najeriya da Gabon
- Rana: 22 Janairu 2022
- Lokaci: 20:00 agogon Kamaru (19:00 GMT)
- Lokaci: Roumde Adjia Stadium, Garoua
Super Eagles ta kawo wannan matakin, bayan da ta ja ragamar rukuni na hudu da maki tara, itace kadai a Kamaru da ta yi nasara a karawar dukkan cikin rukuni, kuma karon farko da ta yi wannan bajintar a Afcon tun 2006.
Najeriya ta fara da doke Masar, sannan ta casa Sudan ta kuma yi nasara a kan Guinea Bissau.
Ita kuwa Tunisia maki uku ta hada a rukuni na shida, bayan da ta yi nasara a hannun Mali da Gambia, amma ta doke Mauritania.
Wannan shine wasa na shida da za su kara a Afcon, hudu daga ciki a matakin sili daya kwale, inda Super Eagles ta yi nasara a uku da canjaras biyu.
Super Eagles ta lashe Afcon karo uku, wato a 1980 da 1994 da kuma 2013, Tunisia kuwa daya ne da ita, wanda ta lashe a 2004 lokacin da ta karbi bakuncin wasannin.
Wasa daya ne Tunisia ta yi nasara a kan Nigeria, shine a 2004 a karawar daf da karshe a bugun fenariti.
Najeriya ta yi nasara a karawa 12 daga 14 da ta yi a Afcon da rashin nasara biyu a Afcon, har da lashe wasa hudu a jere a bayan nan.
Super Eagles ce take da 'yan wasa shida da suka ci mata kwallaye a bana da suka hada da Kelechi Iheanacho da Moses Simon da Simon Chukwueze da Taiwo Awoniyi da William Troost-Ekong da kuma Umar Sadiq.