Afcon 2022: Wasan Morocco da Comoros da Ghana da na Gabon

Asalin hoton, Getty Images
Rukuni na uku zai buga wasa na bibiyu ranar Juma'a tsakanin Morocco da Comoros.
Wasan da za a buga:
Rana: 14 Janairu 2022
Lokaci: 17:00 agogon Kamaru (16:00 GMT)
Filin wasa: Ahmadou Ahidjo Stadium, Yaounde
Wasan rukuni na uku Morocco da Comoros
Wannan shine karon farko da za a kara tsakanin Morocco da Comoros a gasar cin kofin Afirka.
Morocco mai maki uku, bayan da ta ci Ghana a wasan farko ranar Litinin, na fatan yin nasara ta biyu a jere a Afcon, bayan da ta yi wannan bajintar a 2019.
Morocco ta ci wasa shida baya a cikin rukuni a Afcon, wadda ta yi nasara da ci 1-0 a karawa biyar daga ciki.
Watakila Comoros ta zama ta shida da ta fara buga Afcon aka doke ta wasa biyu a jere a cikin rukuni.
Wadanda suka yi rashin kwazon sun hada da Benin (2004), Botswana (2012), Burundi (2019), Niger (2012) and Zimbabwe (2004).
Soufiane Boufal wanda ya ci Ghana a karawar farko ka iya kafa tarihin dan wasan Morocco da ya zura kwallo a raga a wasa biyu a jere bayan Houssine Kharja a 2012 da ya ci kwallo uku jumulla.
Senegal da Guinea
Rana: 14 Janairu 2022
Lokaci: 14:00 agogon Kamaru (13:00 GMT)
Filin wasa: Bafoussam Omnisport Stadium, Bafoussam.
Wasan rukuni na biyu tsakanin Senegal da Guinea
Wannan shine karo na uku da Senegal da Guinea za su kara a tsakaninsu a Afcon, bayan da Sebegal ta yi nasara a wasa biyun.
Senegal ta yi nasara da cin 2-1 a 1994 a karawar cikin rukuni da kuma 3-2 a daf da na kusa da na karshe a 2006, kuma kowanne Guinea ce ke fara cin kwallo.
Senegal ta yi nasara a wasa biyar daga bakwai a Afcon da canjaras daya da rashin nasara a wasa daya.
Guinea na fatan cin wasa biyu a jere a Afcon a karo na biyu, bayan wanda ta yi a 2006.
Sadio Mane yana da hannu a kwallo biyar daga shidan da Senegal ta zura a raga, wanda ya ci hudu ya kuma bayar da daya aka zura a raga.
Wasan Ghana da Gabon:
Rana: 14 Janairu 2022
Lokaci: 20:00 agogon Kamaru (19:00 GMT)
Filin wasa: Ahmadou Ahidjo Stadium, Yaounde
Wasan rukuni na uku Gabon da Ghana:
Ghana za ta fuskanci Gabon, bayan da ta sha kashi a hannun Morocco a wasan farko na cikin rukuni.
Ita kuwa Gabon ta yi nasara a kan Comoros a wasan farko, saboda haka Gabon ta kwan da sanin cewar karawar ba za ta zo da sauki ba.
Ya zama wajibi Ghana ta yi nasara a wasan nan, idan ba haka ba za ta fuskanci barin gasar bana tun daga karawar cikin runi mai kofi hudu jumulla.











