'Yan Barcelona da suka je Granada buga La Liga ranar Asabar

Barcelona FC

Asalin hoton, Barcelona FC

An wallafa

Barcelona ta ziyarci Granada, domin buga wasan mako na 20 a gasar La Liga da za su fafata ranar Asabar.

Wannan shi ne wasa na biyu da Barcelona za ta kara a 2022 a La Liga, bayan da ta doke Real Mallorca 2-1 ranar 02 ga watan Janairun 2022.

Haka kuma shi ne wasa na uku da kungiyar Camp Nou za ta fafata, bayan da ta yi waje da Linares Deportivo da ci 2-1 ranar 5 ga watan Janairu a Copa del Rey, wadda ta ke rike da kofin.

Kungiyoyin biyu sun kara a bana a babbar gasar tamaula ta Sifaniya a Camp Nou, inda suka tashi 1-1 ranar 20 ga watan Satumba.

Granada ce ta fara cin kwallo ta hannun Domingos Duarte a minti na biyu da fara tamaula, daga baya Ronald Araujo ya farke daf da za a tashi daga karawar.

Barcelona tana mataki na biyar a kan teburin La Liga mai maki 31, bayan wasa 19, ita kuwa Granada mai maki 23 tana mataki na 13 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ta bana.

Tuni koci Xavi Hernández ya bayyana 'yan wasa 23 da ya ziyarci Granada da su don buga La Liga ranar Asabar.

Tuni kuma 'yan kwallo takwas suka koma buga wa Barca tamaula da suka hada da Dest da Memphis da Lenglet da L. De Jong da Umtiti da Gavi da Balde da kuma Ez Abde.

Dest da Memphis sun warke daga jinya, yayin da Luuk de Jong bai buga wasan Copa del Rey ba, sakamakon hukuncin dakatarwa.

'Yan wasan Barcelona da za su kara da Granada: Ter Stegen, Dest, Piqué, Sergio, Riqui Puig, O. Dembélé, Dani Alves, Memphis, Neto, Lenglet, L. De Jong, Jordi Alba, O. Mingueza, Umtiti, Eric, Iñaki Peña, Nico, Jutglà, Gavi, Balde, Ez Abde, Álvaro Sanz, I. Akhomach.

Masu yin jinya a Barcelona sun hada da Araujo da Sergi Roberto da Ansu Fati da Frenkie de Jong da Braithwaite da kuma Ferran Torres.

Wasa biyar baya tsakanin Barcelona da Granada:

20/09/21 (La Liga) Barcelona 1-1 Granada

29/04/21 (La Liga) Barcelona 1-2 Granada

03/02/21 (Copa del Rey) Granada 3-5 Barcelona

09/01/21 (La Liga) Granada 0-4 Barcelona

19/01/20 (La Liga) Barcelona 1-0 Granada