Arsenal ta ajiye Pierre-Emerick Aubameyang, saboda rashin da'a - Mikel Arteta

An wallafa

Arsenal ta ajiye kyaftin dinta Pierre-Emerick Aubameyang a gasar Premier League da ta buga da Southampton, saboda rashin da'a in ji Mikel Arteta.

Ranar Asabar Gunners ta doke Southampton 3-0 a wasan mako na 16 a gasar Premier League da suka kara a Emirates.

Aubameyang mai shekara 32 ya yi wa Arsenal karawar da Everton ta yi nasara a babbar gasar Ingila ranar Litinin.

An kuma sa ran dan kwallon tawagar Gabon zai buga wa karawar Southampton ta ziyarci Arsenal a Emirtaes ranar Asabar.

Bayan da aka tashi daga karawar da Arsenal ta yi nasara - Arteta bai yi karin bayani ba kan dalilin da ya ajiye dan wasan.

Athletic ta bayar da rahoton cewar dan wasan ya je latti, bayan da ya kai wata ziyara ba tare da izini ba.

''Dukkan abin da ya faru a dakin canja kaya, ba zan iya sanar da ku ba. kuyi hakuri in ji Arteta.

An kuma tambaye shi ko Arsenal za ta dakatar da Aubameyang, Arteta ya kara da cewar ''ba lamari ne mai dadi ba, ba kuma abin da muke bukata bane a samu kyaftin dinmu cikin wannan halin.

Wannan ba shine karon farko da Arteta ya ajiye Aubameyang ba, saboda hali na rashin da'a.

Ko a watan Maris dan kwallon Gabon din bai yi karawar da Gunners ta doke Tottenham ba.

Aubameyang, wanda ya koma Arsenal kan fam miliyan 56 daga Borussia Dortmund a Janairun 2018, ya saka hannu kan kwantiragin kaka uku a bara a Emirates.

A wannan kakar ya ci kwallo hudu a Premier League - ta karshe da ya zura a raga itace a watan Oktoba a fafatawa da Aston Villa.