Man Utd ya kulla yarjejeniya da Lokomotiv Moscow kan daukar Ralf Rangnick

Ralf Rangnick

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Rangnick ya jagoranci Schalke zuwa wasan dab da na kusa da karshe a gasar Champions League
An wallafa

Kulob din Man Utd ya kulla yarjejeniya da Lokomotiv Moscow kan daukar shugaban wasanni da ci gaba na kulob din Russia Ralf Rangnick domin aiki a matsayin kocin rikon kwarya na Old Trafford.

Ya zuwa yanzu ba a kammala kulla yarjejeniyar ba, saboda wasu bayanai da ake son amincewa da su game da kwangilars kuma akwai bukatar sabon kocin ya samu takardar neman aiki a Ingila.

Sai dai hakan wani batu ne kawai na lokaci kafin Rangnick ya maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a matsayin manajan kulob din zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan kasar ta Jamus, mai shekara 63, zai ci gaba da zama a Old Trafford zuwa shekara biyu domin yin aiki a matsayin mai bayar da shawara.

Rangnick ba zai je United kafin wasan da za su yi da Chelsea ranar Lahadi ba inda Michael Carrick zai ci gaba da jagorsantarsu a matsayi na rikon kwarya.

Carrick ya karbi ragamar kulob din daga hannun Solskjaer, wanda aka sallama daga asiki ranar Lahadin bayan sun sha kashi a hannun Watford da ci 4-1 ranar 20 ga watan Nuwamba.

Carrick, mataimakin Solskjaer, shi ne ya jagoranci kungiyar a wasan da suka doke Villarreal da ci 2-0 ranar Talata.