Kasuwar ƴan ƙwallo: Makomar Hazard a Madrid, Chelsea na son Gavi,

Zlatan Ibrahimovic

Asalin hoton, Gerty images

Bayanan hoto, Zlatan Ibrahimovic
An wallafa

Dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic da alama yana shirin tsawaita zamansa a kulob din na Seria A.

Kwantiragin dan wasan dan kasar Sweden mai shekaru 40, wanda ya koma kungiyar a watan Janairun bara, zai kare a bazara amma zai sanya hannu kan sabon kwantiragi har zuwa watan Yunin 2023. (Football Italia).

Manchester City na dab da sayen dan wasan Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 24, kan fan miliyan 75. (El Chiringuito Via Sun)

Kocin Tottenham Antonio Conte yana sha'awar golan Everton na Ingila Jordan Pickford, mai shekara 27. An ce dan Italiyan na shirin maye gurbin Hugo Lloris mai shekara 35, wanda ke shekarar karshe ta kwantiraginsa a Spurs. (Mirror)

Spurs din na sha'awar dan wasan Bayern Munich da Faransa Corentin Tolisso amma za su iya fuskantar gogayya daga Internazionale kan dan wasan mai shekaru 27. (Kicker - in German)

Gavi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gavi

Chelsea na shirin daukar dan wasan tsakiyar Barcelona Gavi mai shekaru 17.

A halin yanzu, da wuya Chelsea ta ba da aron dan wasan Morocco Hakim Ziyech, mai shekara 28, a watan Janairu. (Telegraph)

Arsenal na son ba wa dan wasan gaban Faransa Alexandre Lacazette, mai shekara 30, kwantiragi na gajeren lokaci domin ci gaba da zama a kungiyar na tsawon kakar wasa. (Mirror)

Roma na iya sake bude tattaunawa don dauko dan wasan Arsenal da Switzerland Granit Xhaka, mai shekara 29. (Corriere dello Sport, via Football 365)

Wakilin dan wasan gaba na Red Bull Salzburg dan kasar Jamus da Liverpool da ke nema Karim Adeyemi, mai shekaru 19, ya gana da Paris St-Germain. (Sport 1 via hanyar Express)

Niklas Sule.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Niklas Sule.

Newcastle United ta samu kwarin gwiwa a zawarcin dan wasan baya na Bayern Munich Niklas Sule. Bajamushen mai shekaru 26 yana son barin kungiyar ta Bundesliga kuma kwantiraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta bana. (Bild, via Sun)

Manchester United ta musanta rade-radin cewa tana son dauko dan kasar Faransa Zinedine Zidane, mai shekara 49 don maye gurbin Ole Gunnar Solskjaer a Old Trafford. (Teleghraph)

Kocin Belgium Roberto Martinez ya yi imanin cewa dan wasan gaba na kungiyarsa Eden Hazard yana "bakin ciki" a Real Madrid. Ana alakanta dan wasan mai shekaru 30 da tsohon kulob dinsa Chelsea da kuma Newcastle. (Metro)

Kocin Burnley Sean Dyche ya ce dan wasan baya na Ingila James Tarkowski, mai shekara 28, "yana da hankali" kuma "ya mai da hankali" duk da sha'awar da Newcastle da West Ham da Tottenham ke yi. (Burnley Express)