Champions League: Abin da ya kamata ku sani kan gasar a kakar 2021-22

Thomas Tuchel

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Ana dab da fara kakar Champions League ta bana wadda kawo yanzu wasu kungiyoyi ke buga karawar cike gurbin shiga gasar 2021-22.

Sai dai kuma tuni an san wadanda suka samu gurbin shiga gasar bana, musamman wadanda sula lashe kofi a gasar da suka buga a bara da wadanda suka mara musu baya.

Kakar bana ta Champions League za ta kunshi kungiyoyi biyar daga La Liga, bayan da Villareal ta lashe Europa League, sakamakon doke Manchester United a kakar da ta wuce.

Kungiyoyin da tuni suka samu gurbin shiga gasar bana:

Tukunyar farko: Chelsea, Villarreal, Manchester City, Atletico Madrid, Bayern Munich, Inter Milan, Lille, Sporting Clube de Portugal.

Tukunya ta biyu: Real Madrid, Barcelona, Sevilla, Juventus, Paris Saint-Germain, Liverpool, Manchester United, Borussia Dortmund.

Tukunya ta uku: Ajax, Leipzig, Atalanta, FC Porto, Zenit.

Watakila a kara a tukunya ta uku:Mai rike da kofi da Besiktas, Dynamo Kiev, Club Brugge.

Tukunya ta hudu: AC Milan, Wolfsburg.

This means that there are still six places up for grabs via the qualification phase, four from the Champions Path and two from the League Path.

Wadanda suka kara a wasannin cike gurbi ranar Agusta 10

Dinamo Zagreb, Legia Warsaw, Cluj, Young Boys, Olympiacos, Ludogorets, Sheriff Tiraspol, Malmo, Rangers, Ferencvaros

Wasannin cike gurbi: Agusta 17-18 da kuma Agusta 24-25

  • Salzburg (AUT) vs Brøndby (DEN)
  • Young Boys (SUI) vs Ferencváros (HUN)
  • Malmö (SWE) vs Ludogorets (BUL)
  • Sheriff (MDA) vs GNK Dinamo (CRO)

Daga nan za a fitar da hudun da za a hada wadanda za a raba jadawalin wasannin cikin rukuni.

Ranar da za a raba jadawalin wasannin bana - Agusta 26

Wasannin cikin rukuni:

  • Wasannin ranar farko - Satumba 14-15
  • Wasannin rana ta biyu - Satumba 28-29
  • Wasanni rana ta uku - Oktoba 19-20
  • Wasanni rana ta hudu - Nuwamba 2-3
  • Wasannin rana ta biyar - Nuwamba 23-24
  • Wasannin rana ta biyar - Disamba 7-8

Karawar kungiyoyi 16, wato zagaye na biyu:

  • Karawar farko - February 15-16 and 22-23
  • Karawa ta biyu - March 8-9 and 15-16

Fafatawar Quarter:

  • Zagayen farko - Afirilu 5-6
  • Zagaye na biyu - Afirilu 12-13

Gumurzun daf da karshe:

  • Wasan farko - Afirilu26-27
  • Wasa na biyu - Mayu 3-4

Ranar wasan karshe:

  • Mayu 28, 2022 a filin wasa na Saint Petersburg