Bahagon 'Yan Sanda ya buge Bahagon Bahagon Kanawa

An wallafa

Bahagon Shagon 'Yan Sanda ya yi nasarar doke Bahagon Bahagon Kanawa a turmi na biyu a damben safe a Dei-Dei, Abuja, Najeriya.

Sauran wasannin da aka yi kisa:

  • Alaye Shagon Sama'ila daga Kudu ya buge Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
  • Dogon Dan Jamilu daga Arewa ya buge Balan Kwarkwada daga Kudu
  • Taufik Shagon Ebola daga Kudu ya buge Shagon Audu Dan Crespo daga Arewa

Damben da bai yi kisa ba kuwa:

  • Shagon Mada daga Kudu da Shagon Dan Tagaye daga Arewa
  • Shagon Gidawe daga Arewa da Shagon Fatalwa daga Kudu
  • Shagon Mustapha daga Arewa da Shagon Shagon Autan Faya daga Kudu
  • Alaye Shagon Sama'ila daga Kudu da Shagon Buhari daga Arewa
  • Biyun Sama'ila daga Kudu da Tafiyar Dan Jamilu daga Jamus.