Bahagon 'Yan Sanda ya buge Bahagon Bahagon Kanawa
An wallafa
Bahagon Shagon 'Yan Sanda ya yi nasarar doke Bahagon Bahagon Kanawa a turmi na biyu a damben safe a Dei-Dei, Abuja, Najeriya.
Sauran wasannin da aka yi kisa:
- Alaye Shagon Sama'ila daga Kudu ya buge Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
- Dogon Dan Jamilu daga Arewa ya buge Balan Kwarkwada daga Kudu
- Taufik Shagon Ebola daga Kudu ya buge Shagon Audu Dan Crespo daga Arewa
Damben da bai yi kisa ba kuwa:
- Shagon Mada daga Kudu da Shagon Dan Tagaye daga Arewa
- Shagon Gidawe daga Arewa da Shagon Fatalwa daga Kudu
- Shagon Mustapha daga Arewa da Shagon Shagon Autan Faya daga Kudu
- Alaye Shagon Sama'ila daga Kudu da Shagon Buhari daga Arewa
- Biyun Sama'ila daga Kudu da Tafiyar Dan Jamilu daga Jamus.