Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mai Takwasara ya buge Bahagon Mancha a damben Abuja
An wallafa
Mai Takwasara ya buge Bahagon Mancha a turmin farko a damben naira 150,000 da suka fafata ranar Lahadi a Abuja, Najeriya.
A cikin watan nan Bahagon Mancha daga Jamus ya doke Mai Takwasara Guramada a jihar n Najeriya.
Wasu wasannin da aka buga a safiyar Lahadin da ba kisa:
- Shagon Autan Faya daga Kudu da Shagon Shagon Mai Takwasara Guramada
- Shagon Shaf-Shaf Guramada da Dan Aliyu daga Arewa
- Shagon Ali Kanin Bello daga Jamus da Biyun Sama'ila daga Kudu
- Dogon Dan Jamilu daga Jamus da Bahagon Sisco daga Kudu
Sai wasan da Shagon Bahagon Sanin Kurna ya buge Shagon Bahagon Fandam