Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gattuso ya bar Fiorentina kwana 22 da bashi aiki
Gennaro Gattuso ya raba gari da Fiorentina, sama da mako biyu da ka nada shi sabon kocin kungiyar.
Ranar 25 ga watan Mayu aka nada tsohon kocin tawagar kwallon kafar Italiya, mai shekara 43 aiki, kuma awa 48 da ya bar jan ragamar Napoli.
Gattuso, wanda ya yi kocin AC Milan, an tsara cewar ranar 1 ga atan Yuli ya kamata ya fara aiki domin fuskantar kakar tamaula da zamu shiga.
Fiorentina ta kammala a mataki na 13 a kasan teburin Serie A a gasar da aka kammala a kakar da ta fara aiki da Giuseppe Iachini daga baya ta koreshi ta maye gurbinsa da Cesare Prandelli, sannan ta kara daukar Lachini.
Wasu rahotanni daga kafafen yada labarai a Italiya sun ce takaddama ce ta barke tsakanin mai Fiorentina dan Amurka, Rocco Commisso da Gattuso kan tsare-tsare ciyar da kungiyar gaba da arzikin da ke kasa wajen sayo sabbin 'yan wasa.
Kawo yanzu ana ta alakanta wasu da ake ganin za sum aye gurbin Gattuso a Fiorentina da suka hada da tsohon kocin Leicester City da Chelsea, Claudio Ranieri da tsohon anda ya horar da Juventus, Andrea Pirlo da kuma dan Faransa, Rudi Garcia.