Bahagon Mai Takwasara ya buge Bahagon Shagon 'Yan Sanda

Bayanan bidiyo, Bahagon Mai Takwasara ya buge Bahagon Shagon 'Yan Sanda
An wallafa

Bahagon Mai Takwasara ya buge Bahagon Shagon 'Yan Sanda a damben naira 150,000 da suka yi a Dei-Dei Abuja, Najeriya

Hakan na nufin Bahagon Mai Takwasara zai karbi naira 100,000 kenan, shi kuwa Bahagon Shagon 'Yan Sanda ya wanke jikinsa da naira 50,000.

Sun buga damben ne a gidan wasa na Ali Zuma da ke Dei-Dei a Abuja, Najeriya a damben Lahadi da safe.