Real ta yi waje da Liverpool a Champions League

Jurgen Kloop

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Liverpool da Real Madrid sun tashi wasa 0-0 a karawa ta biyu zagayen quarter finals a Champions League ranar Laraba da suka kara a Anfiled.

A wasan farko da suka fafata a Spaniya ranar Talata, Real ce ta yi nasara da ci 3-1 da hakan ya kai ta fafatawar daf da karshe a gasar Zakarun Turai ta bana.

Tun farko Liverpool ta fuskanci Real Madrid da shirin cin kwallo biyu idan har tana son zuwa zagayen gaba a Champions League na kakar nan.

Liverpool ta samu damar zura kwallo ta hannun Mohamed Salah karo da dama da kuma Georginio Wijnaldum, sai dai ba ta amfana da hakan ba.

Real Madrid za ta buga karawar daf da karshe da Chelsea wadda ta fitar da FC Porto a wasan da suka yi ranar Talata.

Liverpool wadda ke rike da Premier League tana ta shida a kan teburi da maki 52, kuma saura wasa bakwai ta karkare fafatawar gasar Ingila ta bana.

'Yan wasan Liverpool da na Real Madrid da suka fafata a Anfield ranar Laraba.

'Yan wasan Liverpool da lambar rigunansu:

1. Alisson

66. Alexander-Arnold

47. Phillips

19. Kabak

26. Robertson

5. Wijnaldum

3. Fabinho

7. Milner

11. Salah

9. Firmino

10. Mane

Masu jiran ko-ta-kwana

6. Thiago Alcántara

8. Keita

13. Adrián

15. Oxlade-Chamberlain

20. Jota

21. Tsimikas

23. Shaqiri

28. Davies

46. R Williams

53. Davies

64. Cain

65. Clarkson

'Yan wasan Real Madrid da lambar rigunansu:

1. Courtois

15. Valverde

3. Militão

6. Nacho

23. Mendy

10. Modric

14. Casemiro

8. Kroos

11. Asensio

9. Benzema

20. Vinícius Júnior

Masu jiran ko-ta-kwana

12. Marcelo

13. Lunin

19. Odriozola

22. Isco

24. Mariano

25. Rodrygo

26. Altube

28. Akinlabi Park

30. Arribas

32. Chust