Damben Taufik dogon Ebola da dan Bichi a Abuja

An wallafa

Taukif dogon Ebola ya yi nasarar buge Dogon Inda da ake kira dan Bichi a turmi na biyu ranar Lahadi a DeiDei da ke Abuja, Najeriya.

Wani wasan da aka yi kisa a gidan damben Ali Zuma a safiyar Lahadi shi ne wanda Shagon Lawwalin Gusau ya buge Autan Kugiya.

Damben da aka yi canjaras kuwa:

  • Autan Bila da Autan Ali Kwarin Ganuwa
  • Autan Nuran Dogon Sani da Dogon Na Dada
  • Ilele Shagon Garkuwan Mai caji da Bahagon Alin Tarara
  • Bahagon Bahagon Alin Tarara da Bahagon Bahagon Kanawa
  • Mustaphan dan Shago da Shagon Sojan Kyallu
  • Bahagon Mancha da Bahagon dan Sama'ila