Damben Taufik dogon Ebola da dan Bichi a Abuja
An wallafa
Taukif dogon Ebola ya yi nasarar buge Dogon Inda da ake kira dan Bichi a turmi na biyu ranar Lahadi a DeiDei da ke Abuja, Najeriya.
Wani wasan da aka yi kisa a gidan damben Ali Zuma a safiyar Lahadi shi ne wanda Shagon Lawwalin Gusau ya buge Autan Kugiya.
Damben da aka yi canjaras kuwa:
- Autan Bila da Autan Ali Kwarin Ganuwa
- Autan Nuran Dogon Sani da Dogon Na Dada
- Ilele Shagon Garkuwan Mai caji da Bahagon Alin Tarara
- Bahagon Bahagon Alin Tarara da Bahagon Bahagon Kanawa
- Mustaphan dan Shago da Shagon Sojan Kyallu
- Bahagon Mancha da Bahagon dan Sama'ila