Damben Autan Dan Bunza da Bahagon Bahagon Kanawa

Bayanan bidiyo, Damben Autan Dan Bunza da Bahagon Bahagon Kanawa
An wallafa

Dogon Dan Bunza ya buge Balan Kwarkwada a damben safiyar Lahadi a gidan wasa da ke DeiDei a Abuja, Najeriya.

Da farko kai kace wasan ba zai yi wani kyau ba ashe da saura kallo a gaba, inda Balan Kwarkwada ya bukaci da suyi amarya.

Dogon Dan Bunza ya amsa kowa ya ja daya suka rugu a guje, amma amaryar ba ta yi ba, Balan kwarkwada ya yi korafi Dogo na gudu.

Sai suka sake yin wata amaryar a karo na biyu, suna haduwa kuwa sai ga Balan kwarkwada a kasa sai da 'yan uwa suka taru a kansu sannan ya farfado, bayan da aka yi masa dabaru idan mutum ya suma.

Wasu wasannin da aka yi kisa:

Bahagon Audu Dan Crespo ya buge Abba Dogon Sisco

Taufik ya yi nasara a kan Shagon Sojan Kyallu

Damben da bai yi kisa ba kuwa:

Shagon Soja da Shagon Autan Dan Bunza

Guguwar Mai Takwasara da Bahagon Korona

Autan Dan Bunza da Bahagon Bahagon Dan Kanawa