Greenwood ya tsawaita zamansa a Manchester United

An wallafa

Mason Greenwood ya tsawaita yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Manchester United zuwa karshen kakar 2025.

Cikin kunshin yarjejeniyar dan wasan mai buga gurbin gaba ya amince United ta kara tsawaita zamansa a Old Trafford kaka daya idan ya cika wa'adinsa.

A watan Satumba dan wasan mai shekara 19 ya fara buga wa tawagar kwallon kafa ta Ingila tamaula, kuma yana da kwantiragin da zai kara a United a Yunin 2023 tun farko.

Greenwood ya fara United tun daga matasan kungiyar a lokacin yana da shekara bakwai da haihuwa.

Dan wasan ya ci kwallo hudu a karawa 18 a bana, kuma jumulla yana da kwallo 21 a raga a karawa 82 da ya yi wa Red Devils.

Ole Gunnar Solskjaer ya fara sa Greenwood a babbar kungiyar United cikin watan Maris 2019 yana da shekara 17 da kwana 156 a lokacin.

Greenwood ya fara yi wa Ingila wasa tare da dan kwallon Manchester City, Phil Foden a Nations League da kasar ta doke Iceland 1-0 a watan Satumba.

Daga baya 'yan wasan biyu suka bar sansanin, bayan da suka karya dokar hana yada cutar korona.