Arsenal za ta daukaka kara kan jan katin Luiz

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce kungiyar za ta kalubalanci jan katin da aka bai wa David Luiz a yayin karawarsu da Wolverhampton ranar Talata.
An bai wa Luiz jan kati ne kan ketar da ya yi wa Willian Jose aka kuma bayar da fenariti ga Wolverhampton.
Ruben Nevas ne ya yi bugun daga kai sai mai tsaron raga ya kuma ci kwallon.
Hakan ya sa Arsenal ta sha kashi a gidan Wolverhampton da ci 2-1.
Saura minti 12 a tashi daga karawar alkalin wasa Craig Pawson ya bai wa golan Arsenal, Bernd Leno jan kati, wanda kungiyar ta karasa karawar da yan wasa tara a cikin fili.
Katin shi ne na uku a kungiyar, sai dai Arteta ya ce bai ga dan wasan nasa ya hada jiki da Jose ba.
Mai masukin baki ta kawo karshen wasa bakwai da Arsenal ta yi nasara a gasar ta Ingila.
Da wannan sakamakon Arsenal tana ta 10 a teburin Premier League da maki 31, ita kuwa Wolverhampton mai maki 26 tana ta 14.
Ranar Asabar Arsenal za ta ziyarci Aston Villa a karawar mako na 23 a gasar ta Premier League.











