Coronavirus: 'Yan wasan Man City Jesus da Walker sun kamu

An wallafa

'Yan kwallon Manchester City, Gabriel Jesus da kuma Kyle Walker sun kamu da cutar coronavirus.

'Yan wasan biyu tare da wasu ma'aikatan kulob ɗin su biyu za su killace kansu kamar yadda dokokin gasar Firemiya da na gwamnati suka gindaya.

Hakan na nufin 'yan wasan biyu ba za su buga wa City wasaninta na gaba wato da Newcastle United a ranar 26 ga watan Disamba, da kuma karawa da Everton sai kuma fafatawa da Chelsea a ranar 3 ga watan Janairu.

Ana sa ran Sergio Aguero wanda ya warke daga rauni zai maye gurbin Jesus a cikin tawagar.

A cikin watan Mayu, Walker ya karya dokar kullen korona bayan ya gayyaci wasu karuwai zuwa gidansa.

A halin yanzu dai Manchester City ce ta takwas a kan teburin gasar Firemiya a yayin da ƙungiyar Liverpool ta ba ta tazarar maki takwas.