Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Man United vs PSG: United ce ke jan ragamar rukuni na takwas da maki tara
Ranar Laraba Manchester United za ta karbi bakuncin Paris Saint-Germain a Gasar Champions League karawar rukuni na takwas.
Wasan shi ne na biyar-biyar da kowacce za ta buga a gasar ta cin kofin Zakarun Turai ta bana.
A karawar farko da suka fafata cikin watan Oktoba a Faransa, United ce ta yi nasara da ci 2-1.
Kuma kungiyar Old Trafford ce ta daya da maki tara a rUkuni na takwas, sai Paris St Germain ta biyu da maki shida.
RB Leipzig ma maki shida ne da ita, sai Basaksehir ta hudu da makinta uku.
Manchester United za ta kai zagayen gaba da zarar ta doke Paris St Germain a Old Trafford.
Kuma kungiyar ta Ingila za ta ci gaba da jan ragamar rukuni na takwas idan ta yi nasara a kan PSG, sannan Leipzig ta kasa doke Basaksehir.
United din dai tana da damar jan rukunin ko canjaras ta buga, amma idan aka doke RB Leipzig.
Ita kuwa kungiyar Turkiya, Basaksehir da kyar ne za ta kai zagayen gaba da zarar Leipzig ta yi nasara a kanta,
Kuma Basaksehir za ta ci gaba da zama ta karshe a rukunin da zarar ta kasa cin Leipzig, sannan idan United ba ta doke PSG ba.
Ko kuma da zarar Basaksehir ta yi canjaras, sannan PSG ta yi nasara a kan United za ta dai kare a mataki na hudu a rukuni na takwas.
Saboda haka a ranar Laraba kungiyar United da PSG da kuma Leipzig kowacce tana da damar kai wa zagaye na biyu a gasar ta Champions League ta bana.
Wasanni uku da United ta kara da PSG a gasar Champions League:
Ranar Talata 20 ga watan Oktoba 2020
- Paris St-Germain 1 - 2 Man United
Ranar Laraba 6 ga watan Maris 2019
- Paris St-Germain 1 - 3 Man United
Ranar Talata 12 ga watan Fabrairu 2019
- Man United 0 - 2 Paris St-Germain
Labarin 'Yan wasan Paris St Germain:
Mauro Icardi ba zai buga wasa da United ba, yayin da Marquinhos da kuma Marco Verratti sun murmure za su iya buga fafatawar.
Keylor Navas ya samu sauki zai iya tsaron raga, sai dai kuma 'yan wasa Julian Draxler da Juan Bernat da kuma Pablo Sarabia ba za su buga wasa da United ba.