Kasuwar cinikin 'yan kwallon kafa: Makomar Khedira, Donnarumma, Schuurs, Puig, Thauvin

An wallafa

Dan wasan tsakiyar Jamus Sami Khedira, mai shekara 33, ya ce mai yiwuwa zai tafi kungiyar da ke buga gasar Firimiyar Ingila idan kwangilarsa a Juventus ta kare a bazara mai zuwa. Ya kara da cewa yana tattaunawa da kocin Everton Carlo Ancelotti da na Tottenham Jose Mourinho. (ZDF, via Mail)

Kwangilar golan AC Milan Gianluigi Donnarumma za ta kare a 2021 amma dan wasan na Italiya mai shekara 21 ya ce wakilinsa zai yi magana da kungiyar kuma yana son zama a can na "tsawon lokaci". (Football Italia)

Liverpool na son dan wasan Ajax Perr Schuurs, mai shekara 21, ko da yake har yanzu ba ta tuntubi dan wasan na Netherlands ba. (Voetbal Primeur - in Dutch)

Celtic na son daukar dan wasan Crystal Palace da Jamhuriyar Ireland James McCarthy, sai dai kuma Aston Villa da Burnley su ma suna son dan wasan mai shekara 30. (Teamtalk)

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ba ya hasashen cewa zai sayi 'yan wasa ko kuma wasu 'yan wasansa za su yi gaba idan aka bude kasuwar cinikin 'yan kwallon kafa a watan Janairu. (Evening Standard)

'Yan wasan tsakiya Riqui Puig, mai shekara 21, da Carles Alena, mai shekara 22, suna fafatawa domin ganin sun samu zama daram a Barcelona yayin da shi ma dan wasan Denmark Martin Braithwaite, mai shekara 29, da dan wasan Sifaniya Junior Firpo, mai shekara 24 suke irin wannan fafutuka. (Marca)

Dan wasan Florian Thauvin ya ce ya ji dadi da daraktan wasannin AC Milan Paolo Maldini ya ce masa kungiyar tana son daukarsa. Kwangilar dan wasan mai shekara 27 za ta kare a Marseille a bazarar 2021. (Football Italia)

Mai yiwuwa Juventus ta yi yunkurin daukar dan wasan Atletico Madrid da Montenegro Stefan Savic, mai shekara 29, domin karfafa tsaron bayanta. (Calciomercato)

Tsohon dan wasan Brazil Roberto Carlos ya ce an kulla yarjejeniyar tafiyarsa Chelsea a 2007 sai dai lamarin ya watse a matakin karshe. (Goal)

Barnsley ta matsu ta tsawaita zaman aron dan wasan Leicester City Matty James, a yayin da wa'adin zamansa zai kare a watan Janairu. (Leicestershire Live)