Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Champions League: United ta kuduri ramuwar gayya, Barcelona ta tafi Ukraine
A yau ake dawowa gasar Zakarun Turai ta Champions League, inda Manchester United da Chelsea da Juventus da Barcelona da PSG da dai sauransu za su fafata a zagaye na huɗu na gasar.
Manchester United za ta karbi bakuncin Istanbul Basaksehir ta Turkiya a Old Trafford, a wasan da United din ke shirin rama kashin da ta sha a Istanbul da ci 2-1.
Har yanzu babu tabbacin cewa dan wasan tsakiyar United Paul Pogba ya yi murmurewar da zai iya buga wasan, amma tabbas babu Luke SHaw da Phil Jones da har yanzu ke jinya.
Chelsea kuwa za ta je gidan FC Rennes na Faransa a daren na yau. A wasan da suka buga a Stamford Bridge Chelsea ce ta lallasa Rennes da ci 3-0.
A Sfaniya kuwa, Barcelona ta niƙa gari zuwa Ukraine don fafatawa da Dynamo Kiev.
Barcelona ce ta ci wasan da aka buga a Nou Camp 2-1, kuma ita ce ke jan ragaramar rukunin da maki 9.