Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Zlatan Ibrahimovic: Ya ci kwallo 17 a wasa 22 a gasar kasar Italiya
Zlatan Ibrahimovic ya kara cin kwallo da salon tukin keke da ya bai wa AC Milan damar hada maki uku, bayan doke Udinese a gasar Serie A ranar Lahadi.
Dan wasan mai shekara 39 ya ci kwallo na bakwai kenan a wasa hudu da ya fafata a gasar shekarar nan.
Ibrahimovic - wanda ya ci kwallo 17 a wasa 22 a Serie a karo na biyu da ya koma Milan - shi ne ya bayar da tamaula ga Franck Kessie shi kuma ya fara zura wa a raga.
Daga baya ne Udinese ta farke ta hannun Rodrigo de Paul, a bugun fenariti, bayan da suka koma zango na biyu a fafatawar.
Ibrahimovic ya ci na biyu a salon tukin keke, bayan da ya buga kwallon a tsakanin masu tsaron baya Rodrigo Becao da kuma Sebastian de Maio ta kuma wuce mai tsaron raga, Juan Musso ta fada raga.
Milan ta yi wasa 24 a jere ba a doke ta ba, tun bayan da aka koma taka leda a watan Yuni, bayan jinyar cutar korona.
Cikin watan Maris aka dakatar da wasanni sakamakon bullar annobar.