Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Eriksen da Jones da Isco da Mbappe da Gattuso
Inter Milan a shiirye ta ke ta sayar da ɗan wasan Denmark Christian Eriksen, inda AC Milan da Lazio suka nuna suna buƙatar sayen mai shekara 28 din kan fam miliyan 18 wanda a baya ya buga wa Spurs. (Calciomercato - in Italian)
Mai tsaron baya Phil Jones mai shekara 28 na fargabar ba zai sami tafiya Burnley daga Manchester United ba a watan Janairu saboda ƙungiyar na fuskantar ƙalubale daga masu son sayenta. (Daily Star Sunday)
Isco dan ƙungiyar Real Madrid mai shekara 28 na fatan sake hadewa da tsohon kocinsa Carlo Ancelotti da tsohon abokin wasansa James Rodriguez a Everton. (Sunday Mirror)
Dan wasan baya na na ƙungiyar Malmo kuma ɗn Bosnia, Anel Ahmedhodzic na sha'awar komawa Chelsea, kuma an ce Blues na son biyan fam miliyan 8 domin sayo shi. (Expressen - in Swedish)
Tsohon ɗan wasan Faransa da Arsenal Robert Pires na ganin Kylian Mbappe na Paris St-Germain mai shekara 21 zai fi dacewa da zai koma Real Madrid. (Goal)
Gannaro Gattuso kocin Napoli na daf da sanya hannu kan wata sabuwar kwantiragi domin wadda ke ci za ta shuɗe a karshen kakar wasa ta bana. (Sky Italia - in Italian)
Dan wasan gaba na Atalanta Duvan Zapata na cikin ƴan wasan da Atletico Madrid ke hanƙoron sayowa, kuma koci Diego Simeone na son hada shi da Luiz Suarez. (Calciomercato - in Italian)
Tsohon dan wasan Argentina Diego Maradona ya ce da hali ya ba shi dama, to da ya so ya buga wasa tare da Ian Rush, tsohon dan wasan Liverpool. (Liverpool Echo)
Tsohon dan wasan Bayern Munich da Atletico Madrid da Juventus Mario Mandzukic mai shekara 34 wanda ba shi da kulob a yanzu, an ce ya ki amincewa ya koma Aston Villa.(Birmingham Mail)
Shugaban EFL Rick Parry ya tuhumi ƙungiyar 'yan kwallon ƙafa da jawo cikas ga ayyukan 'ya'yan ƙungiyar bayan da suka gaza taka wa matsalar hauhawan yawan albashin da ake biyansu. (Sunday Telegraph - subscription required)