Juventus: Weston McKennie ya kamu da korona ta killace kanta

An wallafa

Kungiyar Juventus ta sanar cewar ta killace kanta a yammacin Laraba, bayan da Weston McKennin ya kamu da cutar korona.

Mai rike da kofin Serie A, ta ce za ta ci gaba da yin atisaye da buga gasar lig ta Italiya kamar yadda ta saba.

A ranar Talata tawagar kwallon kafa ta Portugal ta sanar da cewar Cristiano Ronaldo ya kamu da cutar korona.

Tuni dan wasan na Juventus ya koma gida domin killace kansa, kuma kafin a gwada dan kwallon bai nuna alamar yana dauke da annobar ba.

Kawo yanzu dukkan 'yan wasan da ba sa dauke da cutar korona za su ci gaba da atisaye a Juventus da buga Serie A, amma ba za su yi mu'amala da wadanda suka kamu da annobar ba.

Kungiyar ta fara killace kanta na kwarya-kwarya ranar 3 ga watan Oktoba, bayan da ma'aikatanta biyu suka kamu da annobar.

Kawo yanzu kungiyar ba ta ce komai ba kan halin da McKennin ke ciki, wanda ya koma Juventus buga wasannin aro daga Schalke 04 a kakar bana.

Ranar Asabar Juventus za ta ziyarci Crotone domin buga gasar Serie A karawar mako na hudu.

Wasannin gasar Serie A da za a ci gaba:

Ranar 17 ga watan Oktoba

  • Napoli da Atalanta
  • Intern Milan da AC Milan
  • Sampdoria da Lazio
  • Crotone da Juventus

Ranar 18 ga watan Oktoba

  • Bologna da Sassuolo Calcio
  • Torino da Cagliari
  • Hellas Verona da Genoa CFC
  • Spezia da Fiorentina
  • Udinese da Parma
  • AS Roma da Benevento

Wadanda ke kan gaba a cin kwallaye a Serie A:

  • Alejandro GomezAtalanta4
  • Andrey Galabinov Spezia 3
  • Francesco Caputo Sassuolo 3
  • Romelu LukakuInter Milan3
  • Cristiano RonaldoJuventus FC3
  • Lautaro MartinezInter Milan 3
  • Rafael LeaoAC Milan 2
  • Luca CaldirolaBenevento2
  • Fabio Quagliarella Sampdoria2
  • Gaetano Castrovilli Fiorentina2
  • Hans HateboerAtalanta 2
  • Hirving Lozano Napoli 2
  • Domenico Berardi Sassuolo 2
  • Jordan VeretoutAS Roma2
  • Gianluca CaprariBenevento2
  • Roberto SorianoBologna FC2