Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Gabriel Jesus: Ɗan wasan Manchester City zai yi jinyar aƙalla mako uku
Dan wasan Manchester City Gabriel Jesus ba zai fafata a karawar da kungiyar za ta yi ta akalla ta mako uku ba.
Tawagar kwallon kafar Brazil ta ce ba zai fafata a wasannin da za ta yi da Bolivia da Peru ba sakamakon raunin da ya ji ranar Litinin a wasan Firimiyar Ingila da suka yi nasara a kan Wolves.
Jesus, mai shekara 23, ya buga wasan minti 90 cif kuma ya zura kwallo.
Dan wasan ya wallafa sako a shafinsa na Twitter cewa: "Zan dawo nan ba da jimawa ba."
"Kungiyar ta Ingila ta tuntubi likitan tawagar kwallon kafar Brazili, Rodrigo Lasmar, inda ta shaida masa halin da dan wasan ke ciki," a cewar sanarwar da tawagar ta fitar.
Shi ma takwaransa na City Sergio Aguero ana sa ran ba zai buga wasa ba nan da karin mako bakwai saboda raunin da ya ji a gwiwarsa.
Brazil za ta fafata da Bolivia ranar 9 ga watan Oktoba sannan ta kara da Peru ranar 13 ga watan na Oktoba.
Man City za ta fafata da Leicester City ranar Lahadi.