Arsenal na son 'fita kunya' a wasan ƙarshe na Cin Kofin FA

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Arsenal ta zaƙu game da wasan ƙarshe na Cin Kofin FA da za ta yi da Chelsea ranar Asabar ɗin nan saboda 'yan wasanta na da burin ganin sun "fitat da mu kunya", in ji Alexandre Lacazette.
Kulob ɗin Gunners, ya lashe Gasar FA 13, inda suka ƙare kakar bana a matsayi na takwas kan teburin Firemiyar Ingila kuma ba za su cancanci zuwa Gasar Europa ba matuƙar suka yi rashin nasara a karawar da za su yi ta filin Wembley.
"Mun ɓaras da 'yan damammakin da muka samu," a cewar ɗan wasan gaban ƙasar Faransa Lacazette, mai shekara 29.
Yayiin da kocin Arsenal, Mikel Arteta da takwaransa na Chelsea, Frank Lampard dukkansu ke hanƙoron cin kofinsu na farko a matsayinsu na koci.
Lacazette ya ƙara da cewa: "Wannan wata bahaguwar shekara ce. Mun tafi dogon hutu, mun canza koci inda Arteta ya maye gurbin Unai Emery a watan Disamba, kuma ga rashin tsayayyun 'yan wasa.
"Kaka ce mai matuƙar wahala, mai yiwuwa wadda ta fi kowacce wuyar sha'ani a shekarun harkar ƙwallona, amma duk da haka na san na koyi ɗumbin abubuwa.
Cin Kofin FA na da matuƙr muhimmanci. Na zo Arsenal ne don cin kofuna."
A lokaci guda kuma, koci Lampard ya goyi bayan ɗan wasan gefen Chelsea Willian ya sake fito da ƙwazonsa na bajinta a karawar ƙarshe da za su yi kafin kwanturagin ɗan ƙasar Brazil ɗin ta ƙare.
"Ya yi mana bajinta. Ya ƙayatar sosai a wannan kaka - ya kuma nuna halaye na ƙwarai," cewar Lampard.

Asalin hoton, Getty Images
Game da ƙungiyoyin
Dan wasan bayan Arsenal Hector Bellerinbai buga wasan da ƙungiyarsa ta yi nasara a kan Watford ba saboda taka-tsantsan da aka yi game da ɗaurewar agararsa amma dai ya dawo atisaye a wannan mako.
Cedric Soares ba zai taka leda a wasan ba saboda ya fara bugawa a wata ƙungiya, yayin da Calum Chambers da Pablo Mari da Shkodran Mustafi da kuma Gabriel Martinelli su ma ba za su buga ba.
Mashahuran tagwayen Chelsea nan N'Golo Kante da Willian na cikin 'yan wasan da za su buga mata bayan dawowarsu daga jinya.
Sai dai, Ruben Loftus-Cheek ya ɗan ji rauni a lokacin atisaye ranar Alhamis don haka an yanke shawarar ajiye shi.

HASASHEN LAWRO
Ba kamar karawar ƙarshe ta bara tsakanin Manchester City da Watford ba, wasan bana da wuya a san maci tuwo, miya ba ta ƙare ba.
Wasa ne da zai kasance wani iri. Mun sani yanzu cewa baƙon abu ne ƙwallon ƙafa ba tare da 'yan kallo ba, amma wannan zai kasance mafi rikitarwa da aka taɓa gani.
Gasar Cin kofin FA ce fa, kuma karawar hamayya, amma ba haka ake kallon lamarin ba. Magoya baya sun zama jini da tsoka a harkar ƙwallon ƙafa, amma an fi ganin muhimmancinsu lokacin da ƙungiya take cin nasara. Kuma ba tare da su ba a wannan kawara ta Wembley, kawai dai za a yi ne.
Duk da haka ina kyautata tsammanin ganin wani wasa mai ƙayatarwa, ko da yake kuma Arsenal ce nake jin za ta yi zarra.
Wannan ba yana nufin cewa Chelsea ba su da hatsari ba ne su ma. Kawai dai ina jin kamar Arsenal sun fi rawar gani ne da kuma ƙwarin gwiwa a yanzu, amma idan ba haka ba, da wuya a iya shiga tsakani.
Bayanai kan haɗuwar ƙungiyoyin
- Arsenal ta cinye duk karawa biyunsu na Cin Kofin FA tsakaninsu da Chelsea a baya: 2-0 a 2002 da kuma 2-1 a 2017.
- Sai dai, Chelsea sun cinye su sauran wasa biyu da suka haɗu a manyan gasanni, da ci 2-1 a Kofin Carling na 2007 da kuma 4-1 a Gasar Kofin Europa na bara.
- Nasara ɗaya kawai da Chelsea ta yi a karawa tara da suka yi da Arsenal a Gasar Kofin FA ta zo ne yayin wasan kusa da na ƙarshe a 2009.











