Coronavirus a Najeriya: 'Akwai yiwuwar sake sanya dokar kulle a ƙasar'
Latsa alamar lasifikar da ke sama domin sauraron tattaunawa da Dakta Sani Aliyu
Jami'in kwamitin shugaban ƙasa da ke yaƙi da cutar korona a Najeriya Dakta Sani Aliyu, ya ce akwai yiwuwar a koma gidan jiya idan 'yan Najeriya suka ci gaba da karya dokar korona.
A tattaunawarsa da BBC ya ce matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na haramta tafiye-tafiye tsakanin jihohi kwata-kwata bai yi aiki ba, ya ce "mutane suna saka kuɗi a aljihunsu su ba jami'an tsaro".
Ya kuma bayyana cewa dalilin da ya sa ake samun yawan lambobi na masu ɗauke da cutar korona a ƙasar na faruwa ne sakamakon ƙara yawan gwajin da ake yi a kullum.
Ya ce a halin yanzu akwai wurare kusan 36 da ake gwajin cutar ta korona, a maimakon huɗu da aka fara da su a farkon ɓullar cutar.
Ya kuma yi bayani kan maganin da aka kai Najeriyar daga Madagascar wanda ake zaton da yana maganin cutar, sai dai da aka yi bincike sai aka gano cewa ya fi ƙarfi wurin maganin Maleriya.
Dakta Sani ya ce a bincikensa, bai ga alamun cewa tazargaden na Madagascar na magance cutar korona ba, sai dai za a ci gaba da bincike a ga ko da yiwuwar zai yi magani.
A halin yanzu dai, yawan mutanen da annobar korona ta shafa a Najeriya sun kai 27,110 kamar yadda hukumar NCDC ta sanar a ranar Alhamis.
Mutum 616 cutar ta kashe sai kuma aka sallami mutum 10,801 tun bayan ɓullar cutar a ƙasar.