'Yan Madrid da suka ci Getafe a La Liga ranar Alhamis

La Liga

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Real Madrid za ta karbi bakuncin Getafe a wasan mako na 33 a gasar La Liga da za su kara ranar Alhamis a filin Alfredo Di Stéfano.

Real tana mataki na daya a kan teburi da tazarar maki daya tsakaninta da Barcelona wacce ta buga 2-2 da Atletico Madrid.

A wasan farko da Real ta je gidan Getafe a kakar bana, ita ce ta yi nasara da ci 3-0 ranar 4 ga watan Janairu.

Getafe ce ta fara cin kanta ta hannun David sannan Raphael Varane ya ci na biyu daga baya Luca Modric ya kara na uku a raga.

Tuni dai kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan kwallo 24 da zai fuskanci Getafe da su.

'Yan Real Madrid da za su fafata da Getafe:

Masu tsaron raga: Courtois da Areola da kuma Altube.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militão da Ramos da Varane da Marcelo da kuma Mendy.

Masu buga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da James da kuma Isco.

Masu buga gaba: Benzema da Bale da Lucas Vázquez da Jović da Asensio da Brahim da Mariano da Vinicius Jr. da kuma Rodrygo.