Jadon Sancho: An ci tarar dan wasan Borussia Dortmund saboda yadda ya yi aski

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafar Jamus ta ci tarar dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho bayan an gan shi a hoto ya yi sabon aski ba tare da amfani da takunkumin fuska ba.
Kazalika an ci tarar takwaransa dan wasa mai shekara 20 Manuel Akanji.
Hukumar kwallon kafar ta ce a fili take cewa sun "keta dokar tsafta da ta kariya daga kamuwa daga cutuka masu yaduwa".
Dortmund ta kare matakin da 'yan wasan suka dauka, tana mai cewa basu keta dokokin kiwon lafiya da na kariya na Bundesliga ba.
Jaridar kasar Jamus Bild ta wallafa labarin a shafinta na Twitter ranar Juma'a dauke da hoton dan wasan.
Ranar Alhamis, daraktan wasanni na Dortmund Michael Zorc ya ce 'yan wasa shida sun tabbatar masa cewa sun bi dukkan dokokin kare kai kuma sun cire takunkumin ne kawai lokacin da za su dauki hoto.
Sai dai hukumar ta dauki matakin cin tarar Sancho da Akanji ne saboda basu sanya tufafin kariya ba.







